Muhammad Malumfashi
20016 articles published since 15 Yun 2016
20016 articles published since 15 Yun 2016
Wani rahoto da aka bankado ya nuna yadda ake zargin ana tafka rashin gaskiya a kwastam. Akwai jami’an kwastam da suka karbi cin hanci amma ana kokarin rufe binciken.
Gwamnati ta kwantar da hankalin ma’aikata a kan rade-radin korar dubbban jama’a daga aiki. Masu cewa za a kori ma'aikata wajen dabbaka aikin Oronsaye sun yi kuskure.
Gwamnan APC ya ba Bola Tinubu shawarar ya binciki Obasanjo kan matsalar wuta. A 1998, Najeriya ta na samar da fiye da megawatt 6, 000 na wutar lantarki.
Kungiyar NLC ta bada wasu shawarwari da bukatu da ‘yan kwadago da sauran takwarorinta su ka dakatar da zanga-zangar lumunar gama-garin da aka shirya.
Ana fatan Isa Pantami ya zama Gwamnan Gombe. Kalubalen farko a gaban malamin shi ne samun tikitin APC, daga nan sai karbuwa a wajen kiristoci da ke Gombe.
A lokacin Muhammadu Buhari, an yi ta buga kudi domin a ba gwamnatin tarayya aro. ‘Yan majalisar dattawa sun nada Sanatoci da za su binciki bashin da Buhari ya karbo.
Ana ta yawo da labarai cewa an ankarar da sojoji a kan shirin kifar da gwamnatin tarayya. Ministan labarai ya ja kunnen masu yada irin labaran nan na bogi.
A sakamakon karbar shawarar kwamitin Stephen Oronsaye, za a taba ma'aikatun gwamnati. Daga cikin wuraren da abin zai iya shafa watakila akwai bankin NEXIM.
Bayan koken koken jama'a, an ji labari CBN ya cigaba da saida Daloli ga ‘yan kasuwar canji. Idan Dala ta fara wadatuwa a bayan fage, farashin Naira zai tashi.
Muhammad Malumfashi
Samu kari