2027: An Cigaba da Kiran Kwankwaso da Obi Su Goyi Bayan Atiku a Kifar da Tinubu

2027: An Cigaba da Kiran Kwankwaso da Obi Su Goyi Bayan Atiku a Kifar da Tinubu

  • Adnan Mukhtar Adam Tudunwada yana so Atiku Abubakar ya sake fitowa neman kujerar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa na 2027
  • Matashin ‘dan siyasar bai ganin Wazirin Adamawa ya tsufa da mulki, a ra’ayinsa shi ne daidai da Mai girma Bola Ahmed Tinubu a takara
  • Legit ta zanta da Adnan Mukhtar Adam Tudunwada wanda ya yi takarar ‘dan majalisa karkashin jam’iyyun UPC da PDP a zabukan baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Adnan Mukhtar Adam Tudunwada, matashin ‘dan siyasa ne daga Kano wadanda ke tare da jam’iyyar adawa ta PDP.

A wata hira da Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya yi da gidan rediyon Freedom a makon nan, ya yi magana zabe mai zuwa.

Atiku
Ana so Atiku ya hadu da Kwankwaso da Obi a 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar, Peter Obi
Asali: Facebook

LP, NNPP za su hadu da Atiku a PDP?

Tsohon ‘dan takaran kujerar majalisar dokokin na Nasarawa a Kano ya kawo shawarar jam’iyyun hamayya su hada-kai.

Kara karanta wannan

"Dino ya tsallake": Tsohon sanatan PDP ya saki satifiket din tsira daga hannun Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adnan Tudunwada yana so Peter Obi na jam’iyyar LP da Rabiu Musa Kwankwaso da ke NNPP su bi bayan Atiku Abubakar a PDP.

‘Dan siyasar ya shaidawa gidan rediyon cewa Atiku Abubakar da ya yi takara a PDP a 2023 ne zai iya kifar da mulkin APC a kasar.

2027: Atiku Abubakar ya fi cancanta

A cikin masu neman mulkin Najeriya, matashin yana ganin Wazirin Adamawa ne yake da karfin arzikin karawa da gwamnati.

Baya ga haka, Adnan Tudunwada ya ce 'dan takaran PDP ne yake fitowa yana sukar manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

"Atiku ne yake tada hankalin APC"

Da Legit ta zauna da Malam Adnan Tudunwada ya shaida mata cewa gwaninsa watau Atiku shi ne dodon jam’iyyar APC a yau.

Cikin sauran ‘yan adawa, yana ganin babu wani wanda yake firgita gwamnatin APC mai-ci kamarsa, don haka yake masa harin 2027.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

Ina batun takarar Kwankwaso a 2027

Yayin da Kwankwasiyya ta kafa gwamnati kuma ta samu kujeru a Kano, Adnan ya ce PDP kuwa tayi kokari a jihohi da yawa.

A hirar da muka yi da shi, ya zargi ‘dan takaran shugabancin kasa na NNPP da yin gum a kan halin da al’umma suke ciki a yau.

Duk da kokarin da NNPP tayi a Kano a 2023, ‘dan adawan yana ganin ci-baya ne jam’iyyun hamayya su bi bayan Kwankwaso.

Ana so Pantami ya nemi takarar 2027

Idan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ji zugar masoyansa, ana da labari cewa kila zai fito takarar kujerar gwamna a zaben 2027.

Ana ba tsohon ministan kasar shawarar ya nemi mulki a zabe mai zuwa, bayan ganin kokarinsa a baya da ya yi ministan tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel