Sojoji Sun Gano Rijiyoyi 40 da Ake Satar Danyen Man Najeriya a Kungurmin Kauye

Sojoji Sun Gano Rijiyoyi 40 da Ake Satar Danyen Man Najeriya a Kungurmin Kauye

  • Sojoji sun ci karo da wani wuri inda aka haka ramuka masu matsakaitan zurfi domin a rika satar danyen man Najeriya
  • Abin da ya ba kowa mamaki shi ne an ci karo da mai a wadannan ramuka, kuma tsageru suna yin abin da suka ga dama
  • Janar Jamal Abdussalam ya shiga da sojoji zuwa Rumuekpe a garin Emohua, aka ga barnar da ake yi wa tattalin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers - Dakarun sojojin kasa da ke Fatakwal har wa yau sun gano wasu rijiyoyi danyen mai sama da 40 da ba a san da su ba.

Rahoton da aka samu a This Day ya ce an gano wadannan rijiyoyi ne a kauyen Rumuekpe a karamar hukumar Emohua a Ribas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu yayi maganar shirin kifar da shi, Sojoji su karbi Gwamnatin Tarayya

Danyen mai
Sojoji da rijiyoyin mai Hoto: Getty Images (Hoton bai da alaka da labarin)
Asali: Getty Images

Sojoji sun gano rijiyoyin mai na sata

A yayin da babban jami’in sojoji na shiyya ta shida, Manjo Janar Jamal Abdussalam ya jagoranci wata shara ne asirinsu ya tonu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Jamal Abdussalam da sauran dakaru suna kokarin kawo karshen barna da ta’adin da ake yi a yankin na Neja Delta a kasar.

A wajen wannan yunkuri aka ci karo da rijiyoyi kimanin 40 wanda fadinsu da tsawonsu ya kai mita 12 sai taku kusan 40 a zurfi.

Barayin mai sun koma hako rijiyoyi

A zantawarsa da manema labarai a wannan wuri, Janar Jamal Abdussalam ya ce barayi sun yi ta haka rami har suka cin ma mai.

Ba kasafai aka saba ganin barayin danyen mai sun yi irin wannan aika-aika ba, babban sojan yake cewa an saba da fasa bututu.

Janar Jamal Abdussalam ya tona asiri

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

"Idan ba ku nan wurin, watakila ba za ku yarda da abin da na ke gani ba."
"A wannan wuri, dakarunmu sun gano ramuka fiye da 40, kuma ramukan nan ba na fasa bututun mai ba ne, hakawa aka yi kamar rijiyoyi"
"Kuma abin ban mamaki, sun samu danyen mai. Ba mu taba ganin irin wannan abin ba."

- Manjo Janar Jamal Abdussalam

Satar danyen mai a N40, 000

Punch ta rahoto jami’in yana cewa sun yi kwanaki biyu suna bincike bayan an kai masu korafin irin asarar da ake yi wa gwamnati.

Jamal Abdussalam ya ce barayin danyen man suna satar arzikin Najeriya ne kamar yadda ake dibar ruwa da guga daga cikin rijiyoyi.

N40, 000 ake biya domin a haka rami, daga nan a shiga satar danyen mai dare da rana a lokacin da ake jiran fara hako mai a Arewa.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su rasa ayyukansu, Shehu Sani ya yi martani kan amincewa da rahoton Oronsaye

Ana kokarin farfado da Naira

A bangaren tattalin arzikin dai, ana da labari CBN ya dage dole sai Naira ta mike a kasuwa, yana yakar wadanda ke jawo tashin Dala.

A makon nan Naira ta cigaba da yin Daraja a kasuwar bayan fage da kuma bankunan kasuwa bayan CBN ya saki fam $300m a bankuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel