Oronsaye: Abin da Zai Faru da Ma'aikatan Gwamnati Wajen Rushe Hukumomi Inji Minista

Oronsaye: Abin da Zai Faru da Ma'aikatan Gwamnati Wajen Rushe Hukumomi Inji Minista

  • Gwamnatin tarayya ta yi karin haske a game da shirin da ake yi na rusa ko narkar da wasu ma’aikatu da hukumomin da ke kasar
  • Ministan labarai da wayar da kai ya ce ma’aikatun da abin zai shafa ba su da amfani ne ko kuwa an samu maimai a aikin na su
  • Alhaji Mohammed Idris ya shaidawa ma’aikata cewa gwamnati ba tayi hakan domin korar ma’aikata ba, sai dai domin yin gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ministan labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ya yi magana a game da aiwatar da aikin kwamitin Steven Oronsaye.

A ranar Laraba, The Nation ta rahoto Mohammed Idris yana cewa mutane ba za su rasa aikinsu saboda an taba ma’aikatun gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnati za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a cikin awa daya, Sheikh Daurawa

Oronsaye
Bola Tinubu ya dauko aikin Oronsaye a gwamnati Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Ministan ya sanar da haka ne a wani jawabi na musamman da ya fitar ta bakin mai taimaka masa wajen yada labarai, Rabiu Ibrahim.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin yin garambawul a ma'aikatun gwamnati

Gwamnati ta ce za a taba hukumomi da ma’aikatun ne saboda a gyara tsarin aikin gwamnati kuma a rage batar da makudan kudi.

A jawabin da ya yi wa manema labarai, ya ce wasu ma’aikatan da za a taba ba su da wani amfani a yau ko dai an samu mai-man aiki.

Oronsaye: Bayanin Ministan labarai a Abuja

"Kwanaki biyu da suka wuce shugaban kasa ya amince da hanyar da za a bi wajen rage kashe kudin tafiyar da gwamnati ta hanyar aiwatar da rahoton Oronsaye – shekaru 12 bayan an gabatarwa shugaban kasa a lokacin, Dr. Goodluck Jonathan."
"Wannan karara ya nuna jajircewar shugaban kasa wajen kula da harkar kudi da tafiyar da gwamnati yadda ta dace ta hanyar sake duban ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu yayi maganar shirin kifar da shi, Sojoji su karbi Gwamnatin Tarayya

- Mohammed Idris

Idris yake cewa sai da gwamnatin tarayya tayi bincike kafin daukar matakin nan. A baya an zarge ta da garajen wajen kawo tsare-tsare.

Ba za a raba mutane da hanyar neman abincinsu ba, za a duba bukatun ‘yan kasa, amma ministan ya ce kishin Najeriya za a sa a gaba.

Oronsaye ba zai sa a rasa aiki ba

An rahoto Sanata Shehu Sani yana cewa amfani da shawarar Steven Oronsaye zai jawo mutane su rasa aiki a gwamnati a kasar.

Tsohon 'dan majalisar ya yarda wannan zai yi maganin facaka da kudi a gwamnati, amma yana tsoron za a talauta wasu masu aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel