Shugaba Tinubu Yayi Maganar Shirin Kifar da Shi, Sojoji Su Karbi Gwamnatin Tarayya

Shugaba Tinubu Yayi Maganar Shirin Kifar da Shi, Sojoji Su Karbi Gwamnatin Tarayya

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya karyata rade-radin da ke yawo cewa sojoji sun fara yunkurin shirya juyin mulki a Najeriya
  • Gwamnatin tarayya ta fitar da jawabi ta bakin Ministan labarai da wayar da kai, inda aka ja-kunne a kan yada jita-jitar nan
  • Mohammed Idris ya ce rahoton ba gaskiya ba ne, wasu ne suke neman birkita kasar kuma za a dauki matakin doka a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kwanan nan aka rika yada jita-jita cewa sojoji sun fara shirye-shiryen hambarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Gwamnatin tarayya ta fito tayi magana a kan batun bayan sojoji sun musanya, The Cable ta kawo rahoton nan a yammacin Talata.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Juyin mulki
Juyin mulki: Minista ya karyata shirin hambarar da Bola Tinubu a Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Gwamnati ta karyata shirin juyin mulki

Ministan harkokin yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris ya fitar da jawabi na musamman, yana karyata wannan magana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Idris ya ce ba za a janye hankalin gwamnati ko a yi mata barazanar da za ta jawo a yi watsi da gyaran da aka kawo ba.

Juyin mulki: Jawabin Ministan yada labarai

"Rahoton wani bangare ne na tunanin masu neman kauda mana hankali, wadanda burinsu shi ne birkita kasar nan kuma su kawo cikas ga gwamnati mai,"
"Yanzu ya fito karara cewa wadannan daidaikun mutane sun komawa buga labaran bogi domin a cire amannar da al’umma suka yi wa gwamnati kuma su dasa tubalin rashin jituwa a kasar nan."

- Mohammed Idris

Za a hukunta masu kawo maganar juyin mulki

Makonni bayan hafsun tsaro ya yi magana, ministan labaran ya ce gwamnati za ta bi doka wajen casa wadanda ke wannan danyen aiki.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

Gwamnati tana ganin cewa masu kawo zancen juyin mulki za su birkita tsaron kasar nan, su kawo barazana ga tsarin mulkin farar hula.

Vanguard ta ce a karshen jawabin ministan, an ja kunnen masu yada irin labaran nan.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga

A wata duniyar, ana da labarin mummunan harin sojoji ya ga bayan wasu jagororin ‘yan bindiga da suka hana jama’a sakat.

Baldo da Baban Yara da yaransu sun yi shekaru suna ta’adi a jejin jihohin Arewa maso yamma, a karshe an hallaka su.

A tashi daya aka rugurguza ‘yan ta’adda kusan 30, majiya ta ce ana so a kawo zaman lafiya a yankin ne kafin damina ta shigo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel