A Karshe Kungiyar NLC Ta Fito Ta Bayyana Gaskiyar Dalilin Tsaida Zanga Zanga

A Karshe Kungiyar NLC Ta Fito Ta Bayyana Gaskiyar Dalilin Tsaida Zanga Zanga

  • Kungiyar kwadago watau NLC ta ce babu irin barazana da matsin lambar da ba ta gani ba saboda shiga zanga-zangar lumana
  • Shugaban ma’aikatan kasar watau Joe Ajaero ya fadi halin da suke ciki a lokacin da ya zanta da manema labarai a garin Abuja
  • Ajaero ya ce an taso su a gaba saboda su janye zanga-zanga, NLC yana zargin ana so a doke su ne sannan a hana su yin kuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyar kwadago ta kasa watau NLC, tayi karin haske a game da dalilin dakatar da zanga-zangar lumanar da ta shirya.

Joe Ajaero wanda shi ne shugaban kungiyar NLC ta kasa ya bayyanawa manema labarai wannan, Tribune ta fitar da labarin a jiya.

Kara karanta wannan

"Dino ya tsallake": Tsohon sanatan PDP ya saki satifiket din tsira daga hannun Tinubu

Kungiyar NLC
Wasu ma'aikata wajen zanga-zangar NLC a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shugaban NLC ya kira taron 'yan jarida

Joe Ajaero ya kira taron manema labarai ranar Laraba a Abuja, ya shaida cewa ana yi wa shugabannin kungiyarsu barazana a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC da wasu kungiyoyin ma’aikata sun yi kwanaki biyu suna zanga-zangar lumana a dalilin halin kunci da wahala da ake ciki a yau.

Ana zargin cewa zanga-zangar ba tayi wani tasiri ba, sai majalisar koli watau NEC ta kungiyar NLC ta bada umarni a dakata haka.

Daily Trust ta rahoto Ajaero yana cewa dole a sanar da al’umma irin barazanar da ake yi wa jagororin kungiyar kwadagon kasar.

NLC tana ganin barazana

"Ana yi mana barazana da matsi domin muyi watsi da abin da tsarin mulki ya ba mu dama ta hanyar gama-garin zanga-zanga."
"An yi mana duk wani nau’in barazana idan muka dage da maganar zanga-zangar."

Kara karanta wannan

Yunwa: Kungiyar kwadago ta dakatar da zanga-zangar gama gari, an fadi dalili

"Amma wannan bai karya mu ba domin wahalar da talakawa da ma’aikatan Najeriya suke ciki bai ba mu wata dama ba."

- Joe Ajaero

Sojoji a sakatariyar kungiyar NLC?

Kwamred Ajaero wanda ya dade yana fafatawa da gwamnatoci ya ce an dauko hayar wasu miyagu domin su birkita zanga-zangar ta su.

A cewar Ajaero, ko lokacin da yake magana, an baza sojoji kan hanyar hedikwatarsu, yake cewa ana son a hana talakawan Najeriya sakat.

A karshen jawabinsa, Kwamred Ajaero ya ce kungiyarsu ta NLC ba za ta ja da baya ba.

Batukatun kungiyar NLC ga gwamnati

Rahoton da muka samu shi ne kungiyar NLC ta fadawa shugaba Bola Tinubu a shigo da abinci da siminti da sauran kaya daga kasar waje.

'Yan kwadago suna so a fasa karin kudin makaranta, a cire VAT kuma a daina karbar haraji a hannun ma’aikata saboda an shiga kunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel