Bankin CBN Ya Dauko Hanyar Fado da Farashin Dala a Kasuwannin Canji

Bankin CBN Ya Dauko Hanyar Fado da Farashin Dala a Kasuwannin Canji

  • Bankin CBN ya dawo cigaba da saida daloli kai-tsaye ga masu harkar cinikin kudin kasashen waje da ake kira BDC
  • ‘Yan canji da ke kasuwar bayan fage za su samu raguwar karancin dala daga yazu, CBN zai rika raba masu fam $20, 000
  • A baya an bar mutane su nemo dalolinsu ne a bankuna saboda CBN yana da karancin daloli a dalilin bashin kamfanoni

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN zai koma cigaba da saida Dalar Amurka a kasuwanni na bayan fage.

Babban bankin ya sanar da haka a wani jawabi na musamman da aka fitar ranar Talatar nan daga birnin Abuja.

Dala.
Gwamnan CBN zai rika saida Dala a BDC Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Sanarwar ta ce kowane ‘dan canjin da bankin ya san da zaman shi zai samu $20,000, Business Day ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

Dalar Amurka: Naira ta tashi a kasuwar canji a sakamakon dabarun Cordoso a CBN

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darektan ciniki da harkar kudin kasashen waje, Dr. Hassan Mahmud ya sa hannu a wannan jawabin da aka fitar.

Naira nawa za a saida Dala a CBN?

Kamar yadda babban bankin na CBN ya sanar da safe, ana saida kowace Dala guda ga ‘dan canji a kan N1, 301.00.

Daily Trust ta ce wannan farashi shi ne ne mafi arahar Dala a kasuwar bayan fage ta NAFEM a halin yanzu.

Kafin a kai ga wannan mataki, ana da labari sai da bankin CBN ya tsabtace yadda ake sana’ar canji a Najeriya.

Dala: 'Yan canji suna koke-koke

Dama mun labari wasu ‘yan kasuwar sun bukaci a dawo saida masu daloli, su kuma su saida ga masu bukata.

"Biyo bayan gyare-gyaren da ake yi a kasuwar canji domin kai wa ga farashin Nairar da te ka daidai da kasuwar,"

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

"Bankin CBN ya lura da yadda ake cigaba da wasa da farashi a hannun ‘yan sari da ke zuwa kasuwar canji."
Wannan yana jawo karin bambancin farashin kudin waje."

- Bankin CBN

A dokar, duk wani ‘dan canji bai isa ya ci ribar sama da 1% a kan kudin da ya saya Dala daga hannun bankin CBN ba.

‘Yan canjin da aka yi wa rajista za su biya kudin da za su saye dala ne a bankunan CBN a Abuja, Awkwa, Legas da Kano.

CBN zai gwabza da Dala

Kuna da labari wanda aka zabo ya rike CBN kwararren masanin tattali ne, ya jagoranci bankuna da kamfanoni.

Yemi Cardoso ya yi aiki da kamfanonin Texaco, Chevron Oil Plc da kuma Cities Alliance Think Tank a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel