Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Dan gwamnan Kaduna, Bashir Nasir El-rufai ya je shafinsa na Twitter domin yiwa Peter Obi da Kingsley Moghalu ba’a, inda ya ce ba za su kai labari ba a 2023.
Wani abun bakin ciki ya afku, inda aka tsinci gawar wasu iyalai su hudu a wani gidan gona a Anguwar da ke karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya, Abuja.
Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda uku a wani hari da suka kai ofishin yan sanda da ke Ishau karkashin Kafin-koro a karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja.
Tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawara a kan tsare-tsaren ritayar shi.
Jam'iyyar All Progressives Congress mai mulki ta tabbatar da cewar babban taronta na kasa zai gudana a ran 26 ga watan Fabrairu kamar yadda ta tsara tun farko.
Sanata Rochas Okorocha ya sa labule da shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu kan aniyarsa ta son zama shugaban kasa a zaben 2023.
Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Masu satar mutanen da suka yi garkuwa da yan uwan malamin jami'ar nan na jihar Zamfara sun nemi a biya su naira miliyan 70 a matsayin kudin fansar sako su.
Wani jagoran kungiyar yan-sa-kai ya CJTF a jihar Borno ya rasa ransa sakamakon fashewar bam da ake zargin yan ta’addan kungiyar Boko Haram da dasawa a Biu.
Aisha Musa
Samu kari