Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari

Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari

  • A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin ritaya a shekarar 2023, Sanata Shehu Sani ya bashi wata muhimmiyar shawara
  • Sani ya ce ya zama dole shugaban kasar ya tsare Kaduna kafin ya sauka daga mulki idan har yana shirin zama a jihar bayan ya yi ritaya
  • A baya dai gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya ce Buhari zai dawo Kaduna da zama ne idan ya kammala wa'adinsa a 2023

Tsohon sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari, shawara a kan tsare-tsaren ritayar shi.

Sani ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnati mai ci ta kawar da ta’addanci da kawo karshen duk wasu nau’i na ta’addanci kafin shugaban kasar ya ji dadin ritayansa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari
Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari
Asali: UGC

A ranar 18 ga watan Disamba ne Buhari yace yana Allah Allah 2023 yayi don ya mika mulki ga sabon shugaban kasa sannan ya koma ga gonarsa.

Hakazalika, a ranar 22 ga watan Disambar bara, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa shugaban kasar zai koma Kaduna da zama ne bayan karshen mulkinsa a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi ga manema labaran fadar Shugaban kasa bayan wata ganawa da Buhari, El-Rufai ya kara da cewa shugaban kasar mazaunin Kaduna ne, duk da cewar ya fito ne daga Daura a jihar Katsina.

Ya ce:

“An gayyaci shugaban kasar domin ya kaddamar da wasu ayyukanmu. Zai shafe kwanaki biyu zuwa uku a Kaduna yana kaddamar da ayyuka a Kafanchan, Kaduna da Zaria.
“Kamar yadda kuka sani, shugaban kasar mazaunin Kaduna ne. Daga jihar Katsina ya fito, amma ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Kaduna. Kuma Kaduna zai koma idan ya yi ritaya.”

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

Sai dai kuma, a wata wallafa da yayi a Twitter a ranar Alhamis, tsohon dan majalisar ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci shugaban kasar ya magance matsalar rashin tsaro idan har yana da shirin zama a Kaduna bayan ya yi ritaya.

Ya rubuta:

“Yan bindiga sun kashe 1,192 sannan sun yi garkuwa da mutum sama da dubu uku a Kaduna a shekarar da ta gabata kawai, fiye da yawan mutanen da aka kashe da sace a Yemen da Libya. Idan har wannan ce jihar da shugaban kasar ke son zama bayan ritaya, toh dole ya fara kare ta.”

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

A wani labari na daban, mun ji cewa gabannin babban zaben 2023, Sanata Rochas Okorocha ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu.

Jaridar Leadeship ta rahoto cewa sanatan ya ziyarci shugaban kasar ne a kan kudirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

A cewar tsohon gwamnan na jihar Imo, ya sanar da Shugaba Buhari cewa ya kamata a saka dukkanin jam’iyyu hudu da suka dunkule suka zama jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a harkokin babban taron jam’iyyar mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel