Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari

Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari

  • Wani dalibin jami'ar ABU da ya kammala karatu kwanan nan, Bashir Maiwada Zubairu ya rasu
  • Zubairu ya rasu ne tare da mahaifiyarsa a wani mummunan hatsarin mota
  • Sun yi hatsarin ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a hanyar Kano zuwa Katsina

Labari da muke samu ya nuna cewa Allah ya yiwa wani dalibin jami'ar Ahmadu Bella University (ABU), Zaria, wanda ya kammala karatu kwanan nan, Bashir Maiwada Zubairu, rasuwa.

A wani wallafa da shafin Instablog9ja ya yi a Instagram, an tattaro cewa Maiwada ya rasu ne tare da mahaifiyarsa a wani hatsarin mota.

Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a hanyar Kano zuwa Katsina.

Dalibin ABU da ya kammala karatu kwanan nan ya rasu tare da mahaifiyarsa a hatsarin mota
Dalibin ABU da ya kammala karatu kwanan nan ya rasu tare da mahaifiyarsa a hatsarin mota Hoto: KossyDerrickEnt
Asali: UGC

Kafin rasuwarsa, marigayin ya karanci fannin injiniya a jami'ar ta ABU kuma ya kasance daya daga cikin dalibai mafi kwazo a ajinsu kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"Abun bakin ciki ne babu Bashir a doron kasa. Ya kasance daya daga cikin manyan daliban injiniya mafi kwazo a lokacinsa. Allahya yafe masa kura-kuransa, ya kuma ji kansu."

Jama'a sun nuna alhini a kan wannan mutuwa tasa.

sheefarh ta yi martani

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun wannan abun bakin ciki ne"

temitope.jimoh ta ce:

Subhana Allah.......Allah ya saka masu da Aljanah fridaus"

yewa_jr ya ce:

"Allah akbar Allah sa Aljannah ya zama makomarsa"

Mutane sun mutu a wani sabon Hatsarin Jirgin ruwa da ya sake aukuwa a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa an tabbatar da mutuwar mutum biyu a wani sabon hatsarin kwalekwalen gargajiya da ya auku a ƙauyen Zangon Durgu, ƙaramar hukumar Rimin Gado, jihar Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun dasa bam a Borno, ya tashi da wani dan-sa-kai

Yace Kwalekwalen, wanda ya ɗauko mutum huɗu kacal, ya kife ne yayin da yake kan hanyar zuwa ƙauyen Kanya daga Zangon Durgu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel