Cikin sauki: Yadda wani mutum ya yi biki mai kayatarwa, ya kashe N20,500 kacal

Cikin sauki: Yadda wani mutum ya yi biki mai kayatarwa, ya kashe N20,500 kacal

  • Wani dan Najeriya, Ani Nnamdi Chris, ya angwance da amaryarsa a wani kasaitaccen biki na sirri
  • Da yake wallafa hotunan bikin wanda aka yi a ranar 4 ga watan Fabrairu, Chris ya ce N20,500 kacal ya kashe a auren
  • Mutumin ya kara da cewar baki 10 kadai aka gayyata ciki harda shi kansa da matarsa inda ya ce sam aure babu tsada

Wani sabon ango mai suna Ani Nnamdi Chris ya bayyana yadda ya angwance da amaryarsa a wani biki na sirri.

Chris ya wallafa hotunan bikin wanda ya gudana a ranar 4 ga watan Fabrairu a shafin Twitter sannan ya bayyana cewa gaba daya abun da ya kashe N20,500 ne – ya biya N15,500 na al’ada da kuma N5,000 na lemu.

Cikin sauki: Yadda wani mutum ya yi biki mai kayatarwa, ya kashe N20,500 kacal
Cikin sauki: Yadda wani mutum ya yi biki mai kayatarwa, ya kashe N20,500 kacal Hoto: @AniNnamdiChris
Asali: Twitter

Ya ce sam aure bai da tsada

A cewar Chris, bayan auren kotun, sai aka yi yar kwarya-kwaryar liyafa inda aka gayyaci mutane 10 kacal ciki harda shi da matarsa.

Kara karanta wannan

Barka: Ministan Najeriya da ya tafi karo ilmi ya kammala Digir-gir a Jami’ar Birtaniya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An daura auren ne a kotun ma’aurata na Port Harcourt yayin da aka gudanar da liyafar a Farrah Coffee Lounge, Port Harcourt.

Ya bayyana cewa bakin da aka gayyata sun kasance yan uwa na kut da kut saboda shi ya zabi yin aurensa cikin sirri.

Ya caccaki wadanda ke tunanin sai an kashe makudan kudi kafin a yi aure inda ya ce:

“Emeka, aure babu tsada, kai ne kake son yin aure kamar mai kudin jini.”

An shiga jimami: Jama'a sun zub da hawaye yayin da amarya ta rasu washe garin aurenta

A wani labarin, mun ji cewa wata kyakkyawar amarya ta amsa kiran mahaliccinta kwana daya bayan an daura mata aure da angonta.

An daura auren amaryar mai suna Hauwa Abdullahi Shehu wacce ake kira da Ummi da angonta ASP Abdulmuhyi Bagel Garba a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, amma sai rai yayi halinsa.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

Shafin mr_mrs_arewa ne ya wallafa labarin mutuwar amaryar a Instagram tare da hoto da katin gayyatar auren nasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel