Muhimmin Tarihi da Tinubu Ya Kafa game da Yaki da Ta’addanci a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya ce sama da mutane 2,000 da ake zargi da ta’addanci na fuskantar shari’a
- Tinubu ya bayyana cewa jami’an tsaron Najeriya sun kashe ko kama hudu daga cikin manyan shugabannin kungiyoyin ta’addanci
- Shugaban ya ce gwamnati na kara karfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro, amfani da fasahar zamani da musayar bayanan sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa sama da mutane 2,000 da ake zargi da ta’addanci na fuskantar shari’a a kasar, yayin da aka samu nasarar yanke wa fiye da mutum 1,000 hukunci.
Shugaban ya ce wannan adadi ya sanya Najeriya cikin kasashen da ke da yawan gurfanar da masu aikata ta’addanci a gaban kotu a duniya.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, a wajen bude taron shekara-shekara na 2026 na Hukumar Leken Asiri ta Tsaro, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Shugaban kasa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28000 da ‘yan sanda 50000 aiki
Ya kuma ce jami’an tsaron Najeriya sun kashe ko kama hudu daga cikin manyan shugabannin kungiyoyin ta’addanci takwas da aka gano a duniya.
Tinubu ya lissafa ‘yan ta’adda da aka kashe, cafke
Shugaban ya ce nasarorin da jami’an tsaro suka samu sun nuna karfin da Najeriya ke da shi wajen tarwatsa shugabancin kungiyoyin ta’addanci da dakile fadadarsu.
Ya bayyana kashe wani babban jagoran kungiyar Islamic State, Abu Bilal al-Minuki, a watan Mayun 2026, da kuma kama Omar Hassan Ma’adou a matsayin wasu daga cikin nasarorin da aka samu.
A cikin jawabin, Tinubu ya kuma ambaci matakan da aka dauka kan kungiyar ISWAP da ke kokarin fadada ayyukanta a kudancin yankin, da kama Abu Barra na kungiyar Ansaru da Mamuda na Mahmudawa a shekarar 2025.
Ya ce jami’an tsaro sun kuma kashe wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga, ciki har da Halilu Sububu, tare da mayakan kungiyoyin da ke barazana ga al’umma.
Sai dai shugaban ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu shugabannin kungiyoyin ta’addanci da jami’an tsaro ke kokarin kamo ko kashewa.
Daga cikinsu akwai Ba Shuwa na ISWAP, Abdullahi Oro na IS-Sahel, Sadiku na JAS a yankin Arewa ta Tsakiya da Bakura Doro a yankin tafkin Chadi.
Tinubu ya tura bukata ga hukumomin tsaro
Shugaban ya bukaci rundunar soji, Hukumar Leken Asiri ta Tsaro, DSS, NIA, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro su kara hadin kai wajen tattara bayanan sirri da dakile ayyukan masu aikata laifuka.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da karfafa alakar tsaro da kasashen Amurka, Faransa, Birtaniya, China, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiyya da sauran kasashen Afirka, cewar Punch.
A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Christopher Musa mai ritaya, ya bukaci jami’an leken asiri su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da himma.
Ya kuma jaddada kudurin gwamnatin tarayya na karfafa masana’antun kera makaman tsaro a cikin gida domin rage dogaro da kasashen waje.
Ta'addanci: An gargadi dillalai, masu haya
An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa duk wanda ya ba ’yan ta’adda gidaje haya zai iya fuskantar hukunci.
NSA ya ce duk wanda ya taimaka wa ’yan ta’adda zai iya fuskantar hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari.
Gwamnati ta kuma yi gargadi ga kamfanonin da ke karbar kudaden da suka shafi ta’addanci, tana mai cewa za a iya ci tararsu Naira miliyan 200.
Asali: Legit.ng

