Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu

  • Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewar babban taronta na kasa zai gudana a ranar 26 ga watan Fabrairu
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ta aikewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu
  • Ta kuma bukaci hukumar INEC ta shirya jami'anta domin su sanya idanu a kan shirin

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da cewar babban taronta na kasa zai gudana a ranar 26 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara tun farko, The Nation ta rahoto.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da kwamitin riko na jam’iyyar APC ta aikewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) domin cika wa’adin kwanaki 21 da hukumar zaben ta gindaya na gudanar da shirin.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu
Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da ranar gudanar da babban taronta na kasa, 26 ga watan Fabrairu Hoto: APC
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an mika wasikar ne a safiyar yau Alhamis, 3 ga watan Fabrairu, a hedkwatar hukumar zaben.

Ci gaban ya kawo karshen rade-radin da ake yi a kafofin watsa labarai cewa kwamitin riko na jam’iyyar na shirin dage ranar gudanar da babban taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasikar mai dauke da kwanan wata 2 ga watan Fabrairu, 2022, dauke da sa hannun shugaban kwamitin rikon, Gwamna Mai Mala Buni da sakatare, Sanata James Akpanudoedehe, ta ce:

“Kari kan wasikarmu ta APC/NHDQ/INEC/19/021/40 mai kwanan wata 11 ga watan Yulin 2021 don sanar da batun gudanar da babban taro na kasa.
“Wannan don sanar da hukumar ne cewa jam’iyyarmu ta shirya gudanar da babban taronta na kasa a ranar Asabar 26 ga watan Fabrairun 2022.
“Wannan sanarwa ce a hukumance kamar yadda yake a karkashin tanadin sashi 85 na dokar zabe (2010) kamar yadda aka gyara.

Kara karanta wannan

NSCDC ta janye jami'an ta da ke tsaron lafiyar dan majalisar da ke so a soke hukumar

“Da fatan za ku shirya jami’anku domin sanya ido a shirin yadda ya kamata."

An tsaurara tsaro a sakateriyar APC yayin da ake rantsar da shugabannin jihohi

A gefe guda, mun ji cewa, a halin yanzu an tsaurara tsaro a sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa dake babban birnin tarayya (FCT).

Wannan mataki na zuwa ne daidai lokacin da Mai Mala Buni, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, zai kaddamar da shugabannin jihohi a yau Alhamis 3 ga watan Fabrairu.

An ga jami’an tsaron dauke da makamai a titin Blantyre a Wuse 2 inda sakateriyar jam’iyya mai mulki take suna tantance mutane da ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel