Wadanda suka sace yan uwan malamin jami’ar Zamfara sun nemi a biya miliyan N70

Wadanda suka sace yan uwan malamin jami’ar Zamfara sun nemi a biya miliyan N70

  • Maharan da suka yi garkuwa da yan uwan malamin jami'ar nan na jihar Zamfara sun nemi a biya su naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa
  • Bukatar tasu na zuwa ne kasa da kwana guda bayan da suka kwashi mutum 5 daga gidan malamin, Abdulrahaman Adamu a yankin Damba a ranar Laraba
  • Mista Abdulrahaman ya tabbatar da cewar maharan sun kira sun kuma nemi a basu kudin, sai dai ya ce a taya su da addu'a

Zamfara - Yan bindigar da suka yi garkuwa da yan uwan wani malamin jami’a a jihar Zamfara sun nemi a biya naira miliyan 70 a matsayin kudin fansar sakinsu.

Wannan na zuwa ne kasa da kwana daya bayan yan bindigar da suka farmaki gidan Abdulrahaman Adamu da ke Damba Quaters, a wajen Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, sannan suka sace mutum biyar.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

Adamu shine shugaban kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ta Jami'ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS).

Yan awanni bayan faruwar lamarin, wata majiya ta iyalin wacce ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewar masu garkuwa da mutanen sun kira su, Channels TV ta rahoto.

A cewarsa, sun bukaci a biya naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa kafin su saki yan uwan nasu.

Hakazalika Mista Abdulrahman ya shaidawa TVC News cewa maharan sun kira suna neman a basu naira miliyan 70 kafin su sako yan uwan nasa.

Ya yi kira da a kara taya shi da addu'o'i domin yan uwansa su dawo gida lafiya.

Majiyoyi sun shaidawa Channels TV cewa maharan sun aiwatar da harin ne a safiyar ranar, inda aka kuma sace wani da ya kasance jami’in jami’ar.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Wadanda aka sace sun hada da kanin shugaban ASUU din, yar kaninsa, dan kaninsa da kannen matansa biyu.

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun dasa bam a Borno, ya tashi da wani dan-sa-kai

A wani labari na daban, mun ji cewa wani jagoran kungiyar yan-sa-kai ya CJTF a jihar Borno ya rasa ransa sakamakon fashewar bam da ake zargin yan ta’addan Boko Haram da dasawa.

Wasu mutane biyar sun kuma jikkata a harin wanda ya afku a karamar hukumar Biu ta jihar Borno, Daily Trust ta rahoto.

Har zuwa mutuwarsa, marigayin, Ibrahim Maliya Saidu shine sakataren tsare-tsare na CJTF a Biu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel