Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

  • An tsinci gawar wani mai gadi da 'ya'yansa su uku a wani gidan gona a a yankin Anguwar da ke karamar hukumar Abaji, Abuja
  • Har ila yau an kwashi matar mai gadin a sume zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abuja
  • Kakakin yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ana nan ana gudanar da bincike

Abuja - Rahotanni sun kawo cewa an tsinci gawar wasu iyalai su hudu a wani gidan gona a yankin Anguwar da ke karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya, Abuja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an samu mai gadin gidan gonan mai suna Dominic Peter Adegeze, yaransa mata biyu, Victoria da Judith da kuma dansa mai wata daya a duniya kwance babu rai.

Kara karanta wannan

Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja
Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja Hoto: Punch
Asali: UGC

Sannan kuma an kwashi matarsa mai suna Laraba wacce take a sume zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abuja, Gwagwalada.

Wani ma'aikacin gidan gonan wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya afku ne a safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Fabrairu, inda ya yi bayanin cewa wani ma'aikaci ya je ba wasu dabobbi abinci a gonar sai ya tarar da ainahin kofar mashigin a rufe da makulli.

Saboda haka sai ya haura katanga sannan ya ga mai gadin da iyalinsa suna nishi da kyar kuma kumfa yana fita ta bakinsu, shafin Linda Ikeji ta rahoto.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ta tabbatar da faruwar lamarin, cewa yan sanda na gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

An kashe jami’an yan sanda uku, an sace mazauna da dama yayin da yan bindiga suka kai hari a Neja

A wani labarin kuma, Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda uku a wani samame da suka kai ofishin yan sanda da ke Ishau karkashin Kafin-koro a karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja.

An tattaro cewa yan bindigar sun kai mamaya ofishin yan sandan su da yawa don sakin wani mai masu kwarmato wanda ke tsare, jaridar The Nation ta rahoto.

Sun kashe jami’ai uku yayin da sauran suka gudu a lokacin harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel