2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

  • Gabannin zaben 2023, Sanata Muhammadu Adamu Alieru ya shiga sahun masu kira ga a mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu
  • Aleiru ya ce bari dan kudu ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari shine zai zamo adalci da daidaito
  • Ya ce tun farko akwai yarjejeniyar da aka cimma a APC kafin Buhari ya hau mulki, cewa bayan ya kammala shekaru takwas, sai a baiwa kudu damar darewa kujerarsa

Kebbi - Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Muhammadu Adamu Alieru ya shiga sahun masu kira ga a mika shugabancin kasar zuwa yankin kudancin Najeriya.

Aleiru ya bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC wanda Vanguard ta sanyawa Ido.

A cewarsa, an gina APC ne a kan tubulin adalci, daidaito da gaskiya, don haka ba daidai bane a ki mika shugabancin kasar ga kudu bayan arewa ta shafe shekaru takwas dinta a kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero
2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero Hoto: Punch
Asali: UGC

Ya ce:

“Akwai yarjejeniyar da aka cimma tun farko kafin Buhari ya zama shugaban kasa, an yarda a Lagas cewa yakamata a marawa Buhari baya don ya yi nasara saboda mutuncinsa, amma a waccan lokacin a wancan lokacin bai da isassun kananan hukumomi da za su kais hi ga lashe zaben shugaban kasa amma saboda yarjejeniyar, APC ta mara masa baya, kuma ya lashe zaben.
“Yanzu a 2023, wa’adin mulkinsa zai kare, don haka adalci da gaskiya shine mika mulki ga kudu kuma bani da matsala da wannan kuma ina goyon bayan haka.”

A yanzu haka ta yi tsami tsakanin dan siyasar na jihar Kebbi da gwamnatin Kebbi kan gudanarwar tarukan APC a jihar yan makonni da suka gabata.

Ya zargi gwamnatin Bagudu da kin bin yarjejeniyar da aka cimma kafin tarukan na sake zabar dukkanin shugabannin jam’iyyar amma sai aka sauke masu yi masa biyayya wanda ke nuna shugabancin jam’iyyar a jihar ya saba matsayar da aka cimma a baya.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Wata sabuwa: Fostocin takarar shugabancin kasa na Amaechi sun karade Daura

A wani labarin, mun ji cewa bayan nadin da Sarkin daura, Faruk Umar Faruk, ya yi wa ministan sufuri, Rotimi Amaechi, fostocin ministan sun karade titunan Daura.

Duk da a wurin nadin sarautar,Mai Martaba ya yi kira da Amaechi da ya nemi babban ofishin shugabancin saboda ya cancanta.

A cewar basaraken, Amaechi ya taka rawar gani wurin kawo jami'ar sufuri Daura kuma titin dogo na Kano zuwa Maradi zai ratsa ta Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel