An shiga jimami: Jama'a sun zub da hawaye yayin da amarya ta rasu ana gab da aurenta

An shiga jimami: Jama'a sun zub da hawaye yayin da amarya ta rasu ana gab da aurenta

  • Allah ya yiwa wata amarya mai suna Hauwa Abdullahi Shehu wacce ake kira da Ummi rasuwa ana hada-hadar aurenta
  • An dai shirya daura auren Ummi ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, amma sai ta ce ga garinku kafin lokacin
  • Labarin mutuwarta ya taba zukatan mutane sosai a shafin soshiyal midiya, inda suka yi mata addu'o'in samun rahmar Allah

Wata kyakkyawar amarya ta amsa kiran mahaliccinta a daidai lokacin da ake shirye-shiryen bikinta.

An dai sanya daurin auren amaryar mai suna Hauwa Abdullahi Shehu wacce ake kira da Ummi da angonta ASP Abdulmuhyi Bagel Garba a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, amma sai rai yayi halinsa kafin ranar.

An shiga jimami: Jama'a sun zub da hawaye yayin da amarya ta rasu washe garin aurenta
An shiga jimami: Jama'a sun zub da hawaye yayin da amarya ta rasu washe garin aurenta Hoto: mr_mrs_arewa
Asali: Instagram

Shafin mr_mrs_arewa ne ya wallafa labarin mutuwar amaryar a Instagram tare da hoto da katin gayyatar auren nasu.

Kara karanta wannan

2023: A mika mulki ga 'yan kudu idan za a yi adalci, inji sanatan Arewa Aliero

lamarin ya afku ne a yankin Azare da ke jihar Bauchi.

Shafin ya rubuta:

"Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun
"Feb 5th
"Dan Allah ku karbi wannan a matsayin jan hankali don yiwa Ummi addu'a. “Allahumma gafirlaha warhamha waafiha wa’afu’anha” Allah ya yafe mata kura-kuranta sannan ya bata jannah."

Labarin mutuwarta ya taba zukatan mutane da dama a shafin soshiyal midiya inda suka ta kwararo mata addu'a cike da nauyin zuciya.

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin sharhin mutanen a kasa:

minalbash_collections ta ce:

"Allahu ya jikanta da rahama yasa aljanna ce makomarta amin"

anchuchi ta rubuta:

"Allah ya jikan ta da rahma "

zainab_biu ta yi martani:

"Allahu Akbar Aure jiya ta innalillahi wa inailaihi raju,u"

fatima_aliyi_ibrahim ta ce:

"Allah yamata rahama❤️❤️❤️"

Kara karanta wannan

Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari

twinzcollections2 ta rubuta:

"ALLAH YA jikanki Ummina"

habibatisamohammed ta rubuta:

"Inna Lillahi wa'ina Ilaihi raji'un. Allah Ya Jikan ta da rahama Ya bada hakuri"

Hadarin mota: Kwanaki bayan kammala digiri a ABU, matashi da mahaifiyarsa sun rasu a hadari

A wani labarin, mun ji cewa Allah ya yiwa wani dalibin jami'ar Ahmadu Bella University (ABU), Zaria, wanda ya kammala karatu kwanan nan, Bashir Maiwada Zubairu, rasuwa.

A wani wallafa da shafin Instablog9ja ya yi a Instagram, an tattaro cewa Maiwada ya rasu ne tare da mahaifiyarsa a wani hatsarin mota.

Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a hanyar Kano zuwa Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel