Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun dasa bam a Borno, ya tashi da wani dan-sa-kai

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun dasa bam a Borno, ya tashi da wani dan-sa-kai

  • Wani bam da mayakan Boko Haram suka dasa ya tashi a karamar hukumar Biu da ke jihar Borno
  • Wani jagoran kungiyar CJTF, Ibrahim Maliya Saidu, ya rasa ransa a harin yayin da wasu mutane biyar suka jikkata
  • Mummunan al'amarin ya afku ne a kusa da kauyen Maliya, gudunmar Mandaragarau a Biu

Borno - Wani jagoran kungiyar yan-sa-kai ya CJTF a jihar Borno ya rasa ransa sakamakon fashewar bam da ake zargin yan ta’addan Boko Haram da dasawa.

Wasu mutane biyar sun kuma jikkata a harin wanda ya afku a karamar hukumar Biu ta jihar Borno, Daily Trust ta rahoto.

Har zuwa mutuwarsa, marigayin, Ibrahim Maliya Saidu shine sakataren tsare-tsare na CJTF a Biu.

Boko Haram: Bam ya tashi da jami’in tsaron ‘dan-sa-kai a Borno
Boko Haram: Bam ya tashi da jami’in tsaron ‘dan-sa-kai a Borno Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a kusa da kauyen Maliya, gudunmar Mandaragarau a Biu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

A cewar wani babban dan CJTF, Mohammed Aliyu, marigayi Maliya ya kasance namijin duniya wanda ya fafata da yan ta’addan a lokuta da dama.

Ya ce:

“Mun samu mummunan labarin a yau da rana, cewa daya daga cikin jaruman mambobin CJTF ya mutu a yayin wani aiki. Abun ya kidima kowa. Allah ya ji kan wanda ya rasu.
“Allah ya kanka danuwana Ibrahim Maliya Saidu Maliya, tare da sauran abokanmu, ciki harda Dakta Suleiman Sykami, wanda ya taka abun fashewa da mayakan Boko Haram suka binne.”

Tashin Hankali: Ɗan Sanda Ya Bindige Soja a Fadar Shehun Borno

A wani labarin, hankula sun tashi a fadar Shehun Borno da ke Maiduguri bayan wani dan sanda, Donatus Vonkong ya harbe sojan da ke aiki da Operation Hadin Kai.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Majiyoyi da yawa sun sanar da Daily Trust a ranar Laraba inda cewa dan sandan ya sha giya ne lokacin.

Matasa sun yi saurin fara farautar ‘yan sanda a wurin amma sojoji sun dakatar da su inda suka ce hakan ba zai kawo gaba tsakanin jami’an tsaron ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel