Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Tsohon ministan sadarwa na Najeriya Olawale Adeniji Ige, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya a ranar Litinin 9 ga watan Mayu, kamar yadda diyar sa ta sanar.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministocinsa da ke neman takarar mukaman shugabanci a 2023 da su yi murabus. Ga jerin sunayen wadanda suka ajiye aiki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, ya bukaci ministocinsa da ke da muradin neman mukaman siyasa gabanin 2023 da su yi murabus.
Babachir Lawal, ya bayyana cewa idan babban jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fadi a zaben shugaban kasa mai zuwa, zai koma gida.
Ministan Kwadago Chris Ngige, ya bayyana cewa zai tuntubi shugaba Muhammadu Buhari da al'ummar mazabarsa kafin ya yi murabus daga majalisar zartarwa ta kasa.
Tsohon sanata mai wakiltan yankin Kano ta arewa, Bello Hayatu Gwarzo, ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na arewa maso yamma.
Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya ya hallaka mutane biyar da jikkata wasu a garuruwan Damaturu, babbar birnin jihar Yobe a yammacin ranar Litinin.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi godiya ga Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano tare da yin rantsuwa da Allah cewa za su rike masa amana.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Sani Yerima, a ranar Talata ya bayyana cewa babu dokar Najeriya da ta kayyade yadda da kuma lokacin da mutum zai yi aure.
Aisha Musa
Samu kari