Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya nuna karfin gwiwar cewa za su kwace mulki a 2023
  • Ayu ya kuma dauki alkawarin cewa za su kashe kudin jam'iyyar cikin hikima tare da bayar da lissafi dalla-dalla
  • A nashi bangaren, Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana cewa za su ba Ayu gudunmawar da ake bukata a matsayinsu na gwamnoninsa

Abuja - Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa suna aiki tukuru don lashe zaben shugaban kasa a zaben 2023.

Ayu ya bayyana hakan ne a daren ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, a yayin wani taro na kwamitin amintattu da kwamitin NEC a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Abubuwa 5 da Tinubu ya ce zai yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu
Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

Shugaban na PDP ya ce mambobin jam’iyyar na aiki ba kakkautawa domin sauya fasalin jam’iyyar da kuma yin zaben fidda dan takarar shugaban kasa mai nasara.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna aiki dare da rana kan bayanai a shirye-shiryen wannan babban taro na musamman.
“Ba wai kawai muna samun hadin kai ba ne, illa muna kara azama wajen yin aiki tukuru da kwato mulki.
“Kowa na aiki tukuru. Na yi imani da wannan za mu taka rawar gani sosai a zabe mai zuwa kuma babu abun da zai hana mu karbar mulki a watan mayun shekara mai zuwa.”

Ayu ya ce kwamitin NWC zai kula da kudaden jam’iyyar yadda ya kamata, rahoton Premium Times.

Ya kara da cewa:

“Za a kashe kudinku cikin hikima, za a yi taka-tsan-tsan wajen kashe kudi kuma za ku san yadda za mu kashe kudadenku. Abun da muke kokarin yi shine inganta wajen sosai don ku zo ku yi taro.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

Da yake magana, Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya ce takwarorinsa za su ba jam’iyyar dukkanin gudunmawar da ake bukata don lashe zaben 2023.

Ya ce:

"Dukkanmu mun shirya sosai don zuwa taruka daban-daban da babban taron kasa, da kuma babban zaben 2023.
“Ina baka tabbacci, mai girma shugaba cewa a matsayinmu na gwamnonin ka, a shirye muke mu ci gaba da baka dukkan gudunmawar da jam’iyyarmu ke bukata don yin nasara a babban zabe, tun daga tarurrukan da za a fara a matakai daban-daban.
“Muna alfahari da aikin da kake yi da na mambobin kwamitin aiki na jam’iyyar.
“Yanzu aka fara aikin sauya fasalin jam’iyyar kuma da izinin Allah tare da kai muna kan hanyar nasara don cetowa da sake gina kasar.”

Shirin 2023: APC ta sake jadawalinta, ta kara wa'adin sayar da foma-foman takara

A wani labarin, jam'iyyar APC ta sake tsawaita wa'adin sayar da fom din takara da sauran shagulgulan da ta sa a gaba gabanin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Akwai aiki: Mai harin Gwamna a APC bai yarda da zabin da Ganduje ya yi na dauko Gawuna ba

Wannan sauyi na zuwa ne daidai lokacin da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka fara mayar da cikakkun foma-foman takara ga jam'iyyar a makon nan.

APC ta kara wa'adin sayar da fom din daga ranar 10 ga watan Mayu zuwa Alhamis, 12 ga watan Mayu, yayin da ta dage mayar da foma-fomai zuwa gobe Juma'a, 13 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel