Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin janyewa, ya bayyana wanda za su marawa baya

Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin janyewa, ya bayyana wanda za su marawa baya

  • Gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Orji Kalu ya ce masu neman takarar shugaban kasa tara za su ajiye kudirinsu
  • Kalu ya ce yan takarar da ya boye sunayensu za su marawa shugaban majalisar dattawa Ibrahim Lawan baya
  • Shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawan ya ce jam’iyyar za ta yi maslaha kan dan takararta tun kafin zaben fidda gwaninta

Abuja - Shugaban masu tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Kalu, ya bayyana cewa yan takarar shugaban kasa tara daga jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) na shirin janyewa daga tseren.

Kalu wanda bai ambaci sunayen masu takarar ba, ya bayyana cewa za su marawa kudirin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan baya, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito.

A ranar Litinin ne Kalu ya janye daga tseren neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa sannan ya nuna goyon bayansa ga Lawan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir

Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin ajiye kudirinsu, bayyana wanda za su marawa baya
Orji Kalu ya ce yan takarar shugaban kasa na APC 9 na shirin ajiye kudirinsu, bayyana wanda za su marawa baya Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Jigon majalisar dattawan ya ce ya yanke hukuncin ne saboda babu tsarin karba-karba a APC kuma an bayar da damar da dukka masu neman takara za su fafata,.

Jaridar The Cable ta nakalto Kalu yana cewa:

“Takarar Lawan zai yadu kamar guguwa.
“Za a sasanta kan batun dan takarar shugaban kasa na APC tun ma kafin ayi zaben fidda gwani.
“A yanzu haka da nake magana, kimanin yan takarar shugaban kasa tara daga jam’iyyarmu sun sanar da ni shirinsu na ajiye kudirinsu don marawa Ahmad Lawan baya.
“Shin hakan bai nuna alamar nasara kafin zaben ba? Takarar Lawan zai yadu kamar guguwa.
“Lawan ya fito daga arewa maso gabas sannan hali daya suke ciki da kudu maso gabas cewa basu samar da shugaban kasa ba tukuna.

Kara karanta wannan

2023: Bafarawa da wasu mutum 4 da su ka hakura da neman Shugaban kasa da dalilansu

“Na maimaita dalilaina na ajiye kudirina saboda Lawan sau da dama kuma na tabbata tuni yan Najeriya suka san da haka.
“Sannan muna sa ran wani gagarumin dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar adawa zai dawo APC.
“Saboda haka, za ku ga cewa jam’iyyar na da nasara sosai kuma a shirye take ta fito da Lawan.”

Kan kira da wasu jam’iyyun siyasa ke yi na a dage zaben fidda gwani, Kalu ya ce baya tsammanin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta saurare su., rahoton Vanguard.

Ya ce an sanar da jam’iyyun a kan lokaci kuma yakamata ace sun shirya sosai kamar yadda hukumar zaben ta bukata.

Mai neman Shugaban kasa a APC ya hakura, Kalu ya fadi wanda yake marawa baya a 2023

A baya mun ji cewa Shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya, Orji Uzor Kalu ya yanki fam domin takarar kujerar Sanata a yankin jihar Abia ta Arewa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Aminu Tambuwal ya nuna karfin gwiwar mallakar tikitin PDP

Daily Trust ta ce Sanata Orji Uzor Kalu ya shaidawa Duniya wannan ne a wani jawabi na musamman da ya saki a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu 2022.

‘Dan siyasar yana cikin wadanda suka fito da farko su na cewa za su yi takarar shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel