Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

  • Fadar shugaban kasa ta magantu a kan dalilin da yasa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya bincikar masu siyan fom din takara na naira miliyan 100 ba
  • Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce hakkin kungiyoyin jama'a da hukumar yaki da rashawa ne su gano tushen kudaden masu takarar
  • Ya kuma bayyana cewa umarnin shugaban kasar na cewa ministoci da sauran masu neman mukamai su yi murabus daga mukamansu bai shafi sashe na 84 na dokar zabe ba

Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban kasar ba zai binciki yadda yan takara suka samu kudaden da suka kashe wajen siyan fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ba.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Channels TV a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Akalla yan takara fiye da 30 ne suka yanki tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, amma Shehu ya bayyana cewa aikin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kungiyoyin jama’a ne gano yadda aka yi suka samu wannan kudi ba wai aikin shugaban kasa ba.

Ya ce:

“Tambayar shine ya aka yi suka samu naira miliyan 100 suka siya fom? Ina ganin ya kamata tambayar ta je ga kowani dan takara ne. Irin wannan bincike ya rataya ne a wuya kungiyoyin jama’a sannan kafafen yada labarai su rika yin tambayoyi, amma suna cewa shugaban kasa ya yi bincike, ba na tunanin wannan ne mafita.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

“Idan ICPC ko EFCC za su ce ‘Ya sakataren dindindin, daga ina ka samu wannan kudin?, shugaban kasar ba zai hana su ba.”

Yakamata a yabawa fom din na naira miliyan 100

A cewar Shehu, yakamata a yabama farashin fom din shugaban kasar na APC domin jam’iyyar na bukatar kudin gudanar da harkokin zabenta.

Ya ce:

“Jam'iyyar ta yi bayani kan wannan batu kuma an yaba wa shugaban jam’iyyar na kasa saboda wannan jam'iyya ce da ba ta karbar kudi daga baitulmalin kasar."

A halin da ake ciki, Shehu ya ce umarnin shugaban kasar na cewa ministoci, shugabannin hukumomi da sauran masu neman mukamai su yi murabus daga mukamansu bai shafi sashe na 84 na dokar zabe ba, Sahara Reporters ta rahoto

"Bai yi magana kan sashe na 84 ba, kawai ya ba da umarnin kuma ina ganin a fili yake cewa a matsayinsa na shugaban bangaren zartarwa na gwamnati, shi ne ke da ikon zartarwa da yanke hukunci.”

Kara karanta wannan

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

Ya kawar da fargabar cewa za a samu baraka a gwamnati biyo bayan umarnin shugaban kasar.

Ya ci gaba da cewa:

“Shugaban ya ba da umarninsa, ya fayyace komai ya rage ga kowa ya kama inda zai je.
"Umurnin da gwamnati ta bayar shine cewa idan kai minista ne kuma kana da karamin minista, ka mika masa mulki. Idan baka da karamin minista, ka mikawa sakataren dindindin.
"Idan kai shugaban hukumar gwamnati ne, jakada, ka mika mulki ga babban jami'i a sashin ka."

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, mun ji cewa za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar Shugaban kasa ya tona asirin masu karyar sayen fam a jam’iyyar APC

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel