Jiga-jigan APC 10 da ka iya maye gurbin ministocin Buhari masu ficewa

Jiga-jigan APC 10 da ka iya maye gurbin ministocin Buhari masu ficewa

  • An umurci ministoci masu ci da ke neman kujerun siyasa da su sauka daga mukamansu ba tare da bata lokaci ba
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayar da umurnin a yayin zaman majalisar zartarwa a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu
  • Umurnin na zuwa ne kwana daya bayan majalisar dattawa ta amince da gyara wani sashin sabon kundin zabe da zai ba zababbun shugabanni damar zama wakilai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, sun bukaci ministocin da ke neman kujerun shugabanci gabannin zaben 2023 da su yi murabus daga mukamansu ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban kasar ya yi umurnin ne a yayin zaman majalisar zartarwa.

Jiga-jigan APC 10 da ka iya maye gurbin ministocin Buhari masu ficewa
Jiga-jigan APC 10 da ka iya maye gurbin ministocin Buhari masu ficewa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnati kuma ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed ya tabbatar da umurnin yayin zantawa da manema labarai bayan taron.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Sai dai idan sun sauya ra’ayinsu, ministocin da lamarin zai shafa sun hada da Abubakar Malami, SAN (Kebbi), Chibuike Amaechi (Rivers), Chris Ngige (Anambra), Timipre Sylva (Bayelsa), Godswill Akpabio (Akwa Ibom), da Ogbonnaya Onu (Ebonyi).

Sauran sune Sunday Dare (Oyo), Pauline Tallen (Plateau), Uche Ogar (Abia), da Emeka Nwajiuba (Imo) – wanda a riga ya yi murabus.

A wannan zauren, Legit.ng ta zakulo wadanda ka iya maye gurbin ministocin a jihohinsu daban-daban.

1. Sanata Adamu Aliero (Kebbi)

2. Sanata Nkechi Nwaogu (Abia)

3. Dr. Kenneth Ugbala (Ebonyi)

4. Cif Amos Gizo (Plateau)

5. Dakuku Peterside (Rivers)

6. John James Akpanudoedehe (Akwa Ibom)

7. Amarachi Iwuanyanwu (Imo)

8. Yekini Nabena (Bayelsa)

9. Sanata Andy Uba (Anambra)

10. Misis Florence Ajimobi (Oyo)

Kara karanta wannan

Da dumi: Malami, Amaechi da sauran Ministocin Buhari dake neman takara sun yi murabus

2023: Ministan Buhari ya bayyana abun da zai yi kafin ya bi umurninsa na yin murabus

A wani labarin, ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr Chris Ngige, ya bayyana cewa zai tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari da al'ummar mazabarsa kafin ya yi murabus daga matsayinsa a majalisar zartarwa ta kasar.

Ministan na martani ne ga umurnin da shugaban kasa Buhari ya bayar a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, cewa dukka mambobin majalisarsa da ke hararar kujerun siyasa a 2023, su yi murabus kafin ranar 16 ga watan Mayun 2022, Leadership ta rahoto.

Ngige, wanda ya yi magana bayan taron majalisar zartarwa a Abuja a ranar Laraba, ya kara da cewar shugaban kasar ya bayar da wata kafa da duk wanda ke neman karin bayani a kan furucinsa zai tuntube shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel