Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir

Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya nuna karfin gwiwar cewa Bola Tinubu zai yi nasara a zaben 2023
  • Ya kuma bayyana cewa duk da yawan yan takarar shugaban kasa a APC sune za su kwashe mafi rinjayen wakilai
  • Sai dai kuma ya bayar da tabbacin cewa Tinubu zai hakura ya koma gida idan har ya fadi a zaben fidda gwanin

Abuja - Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa idan babban jagoran jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fadi a zaben shugaban kasa mai zuwa, zai hakura ya koma gida.

Babachir ya bayyana haka ne a Abuja, a ranar Laraba, 11 ga watan Afrilu, jim kadan bayan wata kungiyar goyon bayansa ta mika fom din takarar shugaban kasa na Tinubu, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari

Tawagar magoya bayan Tinubu karkashin jagorancin gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da Hon. James Abiodun Faleke ne suka mika fom din.

Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir
Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir Hoto: Vanguard

Kungiyar magoya bayan Tinubu ta TSG ce ta siya masa fom din takarar domin shiga tseren tikitin shugaban kasa na APC wanda za a yi a ranar 30 ga watan Mayu.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan mika fom din, tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ya ce koda dai Tinubu na cikin tseren don nasara ne, shi dan damokradiyya ne kuma ba zai tayar da tarzoma ba idan ya sha kaye.

Yace:

“Mun ji dadi cewa a yau mun zo mika fom din nasara kuma mun cika daya daga cikin manyan bukatun jam’iyyar na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC. Mun yi duk abin da ake bukata mun gabatar da duk takardun da ake bukata. Kamar yadda kuke gani, mun sami kwafin takardar amincewar mu kuma muna da tabbacin nasara zai zama namu a ranar 30 ga watan Mayu a yayin babban taron.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

“Mu yan damokradiyya ne kuma mun yarda cewa idan akwai yan takara miliyan daya a karkashin APC mune za mu kwashe mafi rinjayen wakilai a taron. Don haka, duk muna maraba da su. Mun shirya dari bisa dari.
“Babu kalubale. Mu yan siyasa ne, mun kasance a wannan wasan tsawon shekaru masu yawa. Duk kalubalen da zai kasance a wajen, mun riga mun mayar da shi wani dama.
“Asiwaju dan damokradiyya ne. Kada kowani dan siyasa ya tsorata da zaben saboda abu biyu ne zai faru: imma ka yi nasara ko kuma ka fadi. Don haka, idan muka fadi a taron za mu koma gida, mun lashe raunukanmu sannan mu shirya goyon bayan wanda ya yi nasara a tsari na gaskiya da amana.”

Karin bayani: Tinubu ya bayyana abin da zai yi idan ya fadi zaben fidda gwani na APC

A gefe guda, Asiwaju Bola Tinubu, daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki ya magantu kan abin da zai yi idan ya fadi a zaben fidda gwani da jam'iyyar ta shirya yi.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka saboda dalilai

Bayanan na Tinubu na zuwa ne jim kadan bayan da rahotanni suka yadu kan cike ka'ida da ya yi kana da mayar da fom din takarar APC ga shugabannin jam'iyyar.

Ya kuma tabbatar wa mabiyansa cewa zai yi nasara. Sai dai ya ce idan ya sha kashi, zai amince da shan kaye ba tare da wani kurnu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel