Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

  • Iftila'i ya afkawa al'umman wasu garuruwan a garin Damaturu, babbar birnin jihar Yobe, a yammacin Litinin
  • Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya ya halaka mutane biyar sannan ya jikkata wasu da dama
  • Annobar ta kuma lalata gidaje fiye da guda 70, lamarin da ya jefa mutane cikin dimuwa da halin wayyo Allah

Yobe - Akalla mutane biyar ne aka rahoto sun mutu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon ruwan sama da aka tafka a wasu garuruwan Damaturu, babbar birnin jihar Yobe a yammacin ranar Litinin.

Hakazalika, ruwan saman wanda ya fara da misalin karfe 5:30 na yamma sannan ya shafe tsawon awa daya ya lalata gidaje da dama.

Iskan da ya tawo da ruwan saman ya kuma haddasa hatsarurruka da dama yayin da masu motoci suka faka a kan hanya lokacin da suka kasa ganin gabansu.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5
Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wani mazaunin unguwar Sani Daura Ahmed Extension, Abdullahi Umar Bakoro, ya ce ya rasa matarsa da yaransa biyu lokacin da gidansu ya ruguzo sakamakon ruwan saman.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bakoro wanda ya zanta da jaridar Daily Trust a ranar Talata, ya ce ya yi magana da matarsa a kan waya mintuna 15 kafin faruwar annobar.

Ya ce:

“Na ga mutuwa da dama a tsakanin yan uwa da abokaina amma akwai zafi rasa mutumin da kuka yi magana kuma yana cikin koshin lafiya yan mintuna kadan.
“Lokacin da makwabtana suka nemi na gaggauta zuwa gida tsaka da ruwan saman, sai na fahimci cewa ba lafiya ba. Yayin da nake isa gida sai naga kwabcina na kokarin daukarsu zuwa asibiti, abun bakin ciki sun mutu kafin mu isa chan. An binne su a yau.
“Kimanin gidaje 70 abun ya shafa inda wasu suka ruguje sannan wasu rufinsu ya yaye.”

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

Wani mazaunin yankin, Mohammed Sani Bello, ya ce rufin gidansa ne ya yaye amma ya yi sa’a ba a rasa rai ko jikkata ba.

Ya ce yan uwansa suna zama da yan uwa da abokan arziki a wasu wuraren.

“Abu ne mai wahala, wasun mu muna kokawa da abin da za mu ci kafin wannan ibtila’in ya same mu; a halin yanzu mun rasa abun yi a cikin halin kuncin da ake ciki."

Dr Mohammed Goje, babban sakataren hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), ya ce hukumar ta kai dauki ga wadanda abin ya shafa, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Ya ce an kwashe mutane 41 da lamarin ya ritsa da su daga wurare shida zuwa asibiti yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane biyar kuma an sallami mutane 23 daga asibiti.

A halin da ake ciki, Gwamna Mai Mala Buni wanda ya yi umurnin kula da wadanda abun ya ritsa da su a kyauta, ya ziyarci asibitin kwararru na Damaturu inda ya bayar da tallafin kudi ga mutanen.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Gwamnan ya kuma ziyarci gidajen wadanda suka mutu a annobar don yiwa yan uwansu ta’aziyya.

Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bas makare da Fasinjoji bayan Direba ya ƙi jin shawara

A wani labarin, wasu Fasinjoji sun jikkata wasu kuma suka tsallake rijiya da baya bayan wani Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bus ta haya a jihar Legas, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan Direban Motar ya yi kunnen uwar shegu da gargaɗin mutane na ya jinkirta Jirgin da ya kusanto ya wuce.

Lamarin ya faru ranar Talata a kan layin dogo da ya ratsa ta hanyar Ilupeju bye-pass lokacin da Direban Bus Toyota Hiace ya ƙi dakata wa bayan jami'an ba da hannu sun umarci Motoci su tsaya jirgi ya wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel