Da duminsa: Tsohon ministan sadarwa na Najeriya ya mutu

Da duminsa: Tsohon ministan sadarwa na Najeriya ya mutu

  • Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, , Olawale Adeniji Ige, yan kwanta dama a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu
  • Ige wanda ya rasu yana da shekaru 83 a duniya ya rike mukamai da dama a gwamnatin Najeriya baya ga na minista
  • A shekarar 1992, an nada shi a matsayin mai kula da ma’aikatar sufuri, jiragen sama da sadarwa

Iyalan tsohon ministan sadarwa, Olawale Adeniji Ige, sun sanar da mutuwarsa a ranar 9 ga watan Mayu, yana da shekaru 83 a duniya, jaridar The Guardian ta rahoto.

A wani jawabi daga diyarsa, Misis Atinuke Olashore, ta bayyana cewa marigayin ya kasance Darakta Janar na ma’aikatar sadarwa kafin nadinsa a matsayin minister a 1990.

An sake nada shi a matsayin mai kula da ma’aikatar sufuri, jiragen sama da sadarwa a 1992.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Da duminsa: Tsohon ministan sadarwa na Najeriya ya mutu
Da duminsa: Tsohon ministan sadarwa na Najeriya ya mutu Hoto: Guardian
Asali: UGC

A tsakanin 1999 da 2010, Ige ya yi aiki a matsayin mamba na hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ya kuma yi daraktan cibiyar sadarwa a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma kasance mamba a kungiyar bayar da shawara kan harkokin sadarwa ta duniya na farko mai hedkwatarta a Geneva kuma shugaban kamfanin Intanet na Najeriya na farko.

Ige wanda aka haifa a ranar 13 ga watan Oktoban 1938 a Lagas, ya fara aiki tare da kamfanin watsa labarai ta Najeriya, Ibadan a matsayin mataimakin injiniya a 1957 kafin ya tafi Ingila don karantar Injiniyan lantarki a 1961, rahoton The Sun.

Da dawowarsa Najeriya a 1967, ya yada zango a ma’aikatar sadarwa ta tarayya a matsayin injiniya sannan ya daga ya zama Babban Daraktan Gudanarwa na farko, a NITEL sannan ya zama babban manajan kamfanin sadarwa mai dogon zango, a 1985.

Kara karanta wannan

Hotunan Malami Mai Koyar Da 'Yahoo-Yahoo' Da Ɗalibansa 16 Da Aka Kama a Gidan N3m

Jirgin sama makare da mutane ya yi haɗari a Kamaru

A wani labari na daban, wani jirgin sama mai ɗaukar Fasinjoji ya yi haɗari a kusa da babban binrin kasar Kamaru, Yaounde ranar Laraba, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, ma'aikatar kula da harkokin sufuri ta kasar, ta bayyana cewa karamin jirgin saman dake ɗauke da mutane 11 ya yi hatsari ne a wani daji dake Kudu da Yaounde.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzun ba'a gano musabbabin da ya yi sanadin hatsarin, amma wasu bayanai sun bayyana cewa sadarwa ce da datse tsakanin matukin da kuma filin jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel