Auren wuri: Babu doka a Najeriya da ta yi magana kan yadda al'umma za su yi aure, Yeriman Bakura

Auren wuri: Babu doka a Najeriya da ta yi magana kan yadda al'umma za su yi aure, Yeriman Bakura

  • Tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Sani Yerima, ya kare kansa a kan auren karamar yarinya da ya yi
  • Yeriman Bakura ya bayyana cewa bai aikata kowani laifi ba domin babu doka a Najeriya da ta kayyade lokaci da yadda mutum zai yi aure
  • Ya ce hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) ta so yin shari'a da shi a lokacin amma dole ta janye don bai aikata laifi ba

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Sani Yerima, a ranar Talata, 10 ga watan Mayu ya ce babu dokar Najeriya da ta kayyade yadda da kuma lokacin da mutum zai yi aure.

Yerima ya baiwa ‘yan Najeriya da dama mamaki a shekarar 2009 kan zargin yin baiko da wata yarinya ‘yar kasar Masar mai shekaru 13, inda ya biya dala 100,000 ga iyayan amaryar.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Da yake jawabi a yayin wata hira a shirin Politics Today na Channels TV, tsohon gwamnan ya kare abin da ya yi, yana mai cewa bai aikata kowani laifi ba.

Auren wuri: Babu doka a Najeriya da ta yi magana kan yadda al'umma za su yi aure, Yeriman Bakura
Auren wuri: Babu doka a Najeriya da ta yi magana kan yadda al'umma za su yi aure, Yeriman Bakura Hoto: dabofm.com
Asali: UGC

A cewarsa, babu wata al’umma a kasar da ta kayyade shekaru kafin ayi aure.

Sanatan ya yi bayanin cewa an tilastawa hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) wacce tun farko ta nemi a yi masa shari’a janye karar saboda bai yi wani laifi ba.

Ya ce:

“Babu kowani doka a Najeriya da ya kayyade yaushe da yadda mutum zai yi aure. Musulmai na da shari’a, kiristoci ban san menene koyarwarsu ba.
“Da ace na aikata ba daidai ba , da an yi min shari’a a kotu. NAPTIP ta so ta gwada shari’ar sai suka janye maganar saboda ban yi wani laifi ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati ya hango matsala, yace da yiwuwar a fasa zaben Shugaban kasa

“Duk abin da kake yi, idan baka san doka, to tabbas za ka sami matsala. Da zarar kun yi wani abu daidai da doka, ba ka da matsala a koina."

Da aka tambaye shi ko zai duba yiwuwar sake auren karamar yarinya, bai bayar da gamsasshen amsa ba kan haka.

Maimakon haka, ya bayyana cewa a karkashin dokar shari’a, akwai wasu ka’idoji da za a bi kafin ayi aure.

Ya dage kan cewa a koda yaushe doka za ta goyi bayansa domin ba zai taba aikata wani abu da ya sabawa doka ba.

Jigon na APC ya yi alkawarin mayar da albarkatun Najeriya idan ya ci tikitin APC gabanin babban zaben 2023.

Ahmed Yerima: Kiristoci Sun Mori Dokar Shari'ar Musulunci Da Na Kafa a Lokacin Da Na Ke Gwamna a Zamfara

A wani labarin, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Yerima ya ce Kiristocin jiharsa sun amfana kwarai daga dokar musuluncin da ya kafa a jiharsa lokacin ya na gwamna, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

A ranar Talata ya bayyana hakan yayin da Channels Television ta zanta da shi a shirinta na ‘Politics Today’.

Tsohon gwamnan ya ce tun watan Oktoban 1999 ya kafa dokar wacce daga nan sauran jihohin arewa su ka bi sahunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel