An Shirya Yadda Za a Yi Garkuwa da Mbappe, Shugaban Faransa Ya Yi Magana

An Shirya Yadda Za a Yi Garkuwa da Mbappe, Shugaban Faransa Ya Yi Magana

  • An fara binciken wata tawaga da ake zargi da shirin yin garkuwa da fitaccen ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappé
  • Hukumomi sun kama wani matashi mai shekara 18, inda suka gano jerin sunayen mutane 26 da ake zargin sun shirya kai wa hari
  • Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nuna goyon bayansa ga Mbappé, yana cewa babu wanda zai taɓa shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Paris, France - A Faransa, an fara bincike kan wani shiri da ake zargin wasu mutane sun yi na yin garkuwa da fitaccen ɗan wasan ƙasar, Kylian Mbappé.

Lamarin ta tayar da hankula yayin da masoyansa suka bukaci daukar mummunan mataki domin kare rayuwarsa.

Macron ya kare Mbappe da aka shirya sace shi
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: Reuters.
Source: Getty Images

An kama wadanda suka shirya sace Mbappe

A cewar wani bincike da The News ta wallafa, ana zargin ƙungiyar da shirya yin garkuwa da wasu fitattun mutane, ciki har da ɗan wasan Real Madrid.

Kara karanta wannan

An kama Kirista ta yi shigar Musulunci tana satar yara a Abuja

Hukumomin Faransa sun kama Clement L, wani matashi mai shekara 18, ranar Laraba, bayan an tuhume shi tare da wani abokin aikinsa.

An tuhumi mutanen ne a ranar 21 ga Agusta a Nanterre kan zargin aikata fashi cikin tsari da kuma wasu laifuka masu nasaba da aikata manyan laifuka.

A cewar masu bincike, ana danganta ƙungiyar da wasu hare-haren mamaye gidaje da kuma shirye-shiryen yin garkuwa da mutane tsakanin watan Afrilu da Agusta 2026.

Daga cikin muhimman shaidun da jami’an tsaro suka samu akwai wayoyin hannu guda biyu da aka kwace daga gidan yari, cewar Marca.

Binciken wayoyin ya taimaka wajen gano wani jerin sunayen mutane 26 da ake zargin ƙungiyar ta sanya a matsayin waɗanda za ta iya kai wa hari.

Jerin ya ƙunshi ’yan kasuwa, wani fitaccen mutum a masana’antar kiɗa ko mawaki, da kuma shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa Kylian Mbappé.

Sai dai har yanzu babu tabbacin cewa an aiwatar da wani shiri na musamman domin yin garkuwa da Mbappé ko kuma kai masa hari.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke likitoci, lauyoyi da masu ba 'yan bindiga bayanai

Macron ya bayyana muhimmancin Mbappe
Kylian Mbappe da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: FRANCK FIFE / AFP.
Source: Getty Images

Macron ya mayar da martani

Bayan kama wanda ake zargi da kasancewa cikin shirin da ake dangantawa da Mbappé, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya mayar da martani kan lamarin.

Macron ya wallafa wani saƙo da The Sunday Guadian ta ruwaito, ya bayyana matuƙar goyon bayansa ga ɗan wasan na Faransa.

Ya ce:

“Yunƙurin SACE Kylian Mbappé? BABU WANDA ZAI IYA TAƁA KYLIAN. Ya saka rigar tawagar Faransa. Shi kadarar ƙasa ne.”

Lamarin ya ƙara jawo hankali kan matsalar tsaro da ke fuskantar fitattun ’yan wasa, musamman waɗanda suka yi suna a duniya.

A halin yanzu, binciken hukumomin Faransa na ci gaba domin gano cikakken shirin ƙungiyar da kuma ko tana da niyyar kai hari ga Mbappé.

Kylian Mbappé na daga cikin fitattun ’yan wasan ƙwallon ƙafa na zamaninsa, inda ya samu manyan nasarori tare da tawagar Faransa.

Za a karrama Messi bayan ritaya a Argentina

An baya, an ji cewa hukumar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta za ta karrama shahararren dan wasa Lionel Messi wanda ya yi ritaya daga taka wa kasarsa leda.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa Argentina wasa bayan ya ce wasan ƙarshe da Spain a gasar Kofin Duniya ta 2026 shi ne na ƙarshe.

Dan wasan ya buga wa Argentina wasa a Kofin Duniya guda shida, inda ya lashe gasar a 2022 tare da kafa tarihin zura ƙwallaye 125 wa ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.