Hanyar da Argentina Za Ta Karrama Messi bayan Ritaya daga Taka Mata Leda

Hanyar da Argentina Za Ta Karrama Messi bayan Ritaya daga Taka Mata Leda

  • Hukumar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta za ta karrama shahararren dan wasa Lionel Messi wanda ya yi ritaya daga taka wa kasarsa leda
  • Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa Argentina wasa bayan ya ce wasan ƙarshe da Spain a gasar Kofin Duniya ta 2026 shi ne na ƙarshe
  • Messi ya buga wa Argentina wasa a Kofin Duniya guda shida, inda ya lashe gasar a 2022 tare da kafa tarihin zura ƙwallaye 125 wa ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Buenos Aires, Argentina - Hukumar ƙwallon ƙafa ta Argentina (AFA) ta sanar da shirin karrama fitaccen ɗan wasan ƙasar, Lionel Messi, a ƙarshen wannan mako.

Hukumar ta ce za a dakatar da wasannin ƙwallon ƙafa na cikin gida a minti na 10 na rabin farko, domin ’yan kallo su yi wa Messi tafi na tsawon minti ɗaya.

Kara karanta wannan

Daliban ABU Zaria sun kera na'urar da makafi za su rika tafiya da ita cikin salama

Argentina za ta karrama Messi
Lionel Messi na murnar zura wa Argentina kwallo Hoto: leomessi
Source: Getty Images

An shirya wannan karramawa ne domin girmama tarihin da Messi ya yi yayin da yake wakiltar ƙasar Argentina a matakin ƙasa, cewar rahoton BBC.

Karramawar za ta shafi dukkan rukuni

AFA ta bayyana cewa za a gudanar da wannan karramawa a wasannin dukkan rukunan maza da mata da kuma sauran fannoni da ke ƙarƙashin hukumar.

A cikin sanarwarta, hukumar ta ce:

“A wasannin da ke tafe na dukkan rukunan maza da mata da fannoni, za a dakatar da wasa a minti na 10 na rabin farko domin tafi na tsawon minti ɗaya don girmama tarihin Lionel Messi da ƙungiyar Argentina.”

Hukumar ta kuma umarci filayen wasan da ke da allunan bidiyo da su nuna wani faifan bidiyo na musamman domin karrama Messi kafin a fara wasanni.

Za kuma a wallafa wannan faifan bidiyon a shafukan sada zumunta na hukumar.

Messi ya kafa tarihi da Argentina

Messi ya fara buga wa babbar ƙungiyar Argentina wasa ne a shekarar 2005, inda daga baya ya zama ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin ƙasar.

Kara karanta wannan

INEC ta fadi abin da ake tsoro ya hana zaben 2027 zama sahihi

Ya ci wa Argentina ƙwallaye 125, sannan ya wakilci ƙasar a gasar Kofin Duniya sau shida.

A shekarar 2022, Messi ya jagoranci Argentina zuwa lashe Kofin Duniya, inda ƙasar ta kawo ƙarshen dogon jiran shekaru 36 ba tare da lashe gasar ba.

Dan wasan mai shekaru 39 a yanzu yana riƙe da wasu manyan tarihin Kofin Duniya, ciki har da yawan wasannin da ɗan wasa ya buga, wato 34, da kuma yawan nasarorin da ya samu, wato 23.

Messi ya sanar da ritayarsa

Messi ya sanar da matakin yin ritaya daga buga wa Argentina wasa ta shafinsa na Instagram. Ya rubuta cewa:

“Na ba da duk abin da nake da shi; babu abin da ya rage da zan bayar.”

“Mataki ne wanda ya yi mini zafi, kuma har yanzu yana ciwo a cikin zuciyata, amma na fahimci cewa lokaci ya yi.”

Tarihin da Messi ya kafa a Argentina

Baya ga lashe Kofin Duniya a 2022, Messi ya taimaka wa Argentina wajen samun nasara a gasar Copa América, lamarin da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a tarihin ƙwallon ƙafar ƙasar.

Kara karanta wannan

An samu kasar da ta yanke hulda da Iran ana tsaka da yaki da Amurka

Tarihin Messi da Argentina ya sa ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan da suka taɓa wakiltar ƙasar a duniya.

Messi ya yi ritaya daga buga wa Argentina wasa
Lionel Messi bayan wasan karshe na Argentina a gasar kofin duniya Hoto: leomessi
Source: Instagram

Mahaifin Messi ya mutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mahaifin Lionel Messi, Jorge Messi, ya yi bankwana da duniya yana da shekaru 68 a duniya.

Jorge Messi ya mutu ne a wani asibitin musamman da ke Rosario, Argentina, bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng