An Kama Kirista Ta Yi Shigar Musulunci Tana Satar Yara a Abuja
- Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sake kama wasu tsofaffin fursunoni biyu bisa zargin satar yara da safarar su
- An kama Rose Daniel da Blessing John ne a ranar 27 ga Agusta, 2026, yayin da ake zargin suna kokarin tserewa da wata yarinya
- Kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta ce an kama wadanda ake zargin ne bayan samun sahihin bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta sake kama tsofaffin fursunoni biyu bisa zargin yin garkuwa da yara da safarar su zuwa wasu sassan Najeriya.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa an kama Rose Daniel da Blessing John ne a ranar 27 ga Agusta, 2026, yayin da suke kokarin tserewa da wata yarinya ‘yar shekara hudu.

Source: Facebook
An ceto yarinyar a Kuje
Rahoton Vanguard ya nuna cewa Adeh ta ce jami’an ‘yan sanda sun isa wurin cikin gaggawa bayan wani mutum mai damuwa ya sanar da su abin da ya faru.
Ta ce jami’an sun ceto yarinyar, Ummi Mariam Abdullah, tare da kama wadanda ake zargin:
“Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka ceto yarinyar tare da kama wadanda ake zargin,”
Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin an taba kama su a watan Disamba na 2025, inda aka gurfanar da su a gaban kotu kan makamancin wannan laifi.
An same su da laifi a baya
A cewar Adeh, kotu ta same su da laifi sannan aka sake su bisa beli bayan sun shafe kusan wata biyar a gidan yari.
Ta ce bayan an sake su, binciken ‘yan sanda ya nuna cewa ana zargin mutanen biyu da sake satar yara tare da safarar yara hudu zuwa wurare daban-daban a Najeriya.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun sauke fushin abin da jami'an tsaro suka masu kan manoma a Sakkwato
Ta bayyana cewa lamarin baya-bayan nan ya shafi yara biyu da ake zargin an kai su wurin wata abokiyar huldar su da ke Fatakwal, wadda aka bayyana da suna Madam Ijeoma.
Yadda suke sayar da yara
Adeh ta ce Madam Ijeoma da ake zargin abokiyar huldar wadanda ake zargin ce, ta sayi yaran biyu kan Naira miliyan 1.5 kowanne.
Ta ce yarinyar da aka ceto, Ummi Mariam Abdullah, an mayar da ita hannun iyalanta, yayin da wadanda ake zargin ke tsare a hannun ‘yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.

Source: Original
Ta kuma bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani mutum, motsi ko aiki da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Rundunar ta ce ana iya kiran layukan gaggawa 08032003913 da 08028940883, ko Sashen Kula da Korafe-korafen Jama’a ta lambar 08107314192, yayin da za a iya tuntubar PPRO na FCT ta 07038979348.
Ga bidiyon matar da aka kama sanye da hijabi da Babangida ya wallafa a X:
Maganar tsaro a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya yi Allah-wadai da hare-haren ‘yan bindiga da aka kai a kananan hukumomi hudu na jihar.

Kara karanta wannan
Ta faru ta ƙare: Sojoji sun shiga maɓoyar ƙasurgumin ɗan bindiga, Kachalla Muhammadu
Wuraren da lamarin ya shafa sun hada da Chiromawa a karamar hukumar Garun Mallam, Beli a Rogo, Bebeji da kuma wasu al’ummomi da ke kusa da Gwarzo.
Gwamnan ya jajanta wa wadanda hare-haren suka rutsa da su da iyalansu, tare da tabbatar musu cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da jami’an tsaro.
Asali: Legit.ng
