Daliban ABU Zaria Sun Kera Na'urar da Makafi za Su Rika Tafiya da Ita cikin Salama

Daliban ABU Zaria Sun Kera Na'urar da Makafi za Su Rika Tafiya da Ita cikin Salama

  • Wasu ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria (ABU) sun ƙera wata sabuwar sandar tafiya ta zamani domin taimaka wa wadanda ba su gani
  • Na’urar tana amfani da na’urorin gano cikas, ramuka da ruwa, inda take faɗakar da mai amfani ta hanyar girgiza da sautuka daban-daban
  • Sandar ta kuma ƙunshi katin SIM, wanda ke ba mai amfani damar aika saƙon SMS zuwa ga wanda aka yi wa rajista a matsayin mai kula da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Zaria – Wasu ɗaliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria (ABU) sun ƙera wata sandar tafiya mai amfani da fasahar zamani domin taimaka wa makafi wajen gane abubuwan da ke gabansu.

Bidiyon da ke nuna yadda na’urar ke aiki ya ja hankalin jama’a bayan an wallafa shi a shafin X ranar 2 ga Satumba, 2026.

Kara karanta wannan

An bukaci Tinubu ya hakura da shiga takara a zaben 2027

Dalibana jami'ar ABU Zariya
Daliban da suka kirkiro na'urar. Hoto: @Umaikanoh
Source: UGC

Shafin Abuinsight ne ya wallafa bidiyon a X, inda aka ga ɗaya daga cikin ɗaliban da suka ƙera na’urar yana gabatar da ita a wajen taro tare da bayyana yadda kowanne daga cikin tsarin sandar ke aiki.

Yadda sandar ke taimakon makafi

Rahoto ya nuna cewa wasu ɗaliban aji 300 na fannin kimiyyar Kwamfuta a jami'ar ABU ne suka kera sandar.

Na’urar tana amfani da tsarin na’urori masu auna abubuwa domin gano nau’o’in haɗari daban-daban da mai amfani zai iya fuskanta yayin tafiya.

Idan sandar ta gano wani abu mai ƙarfi a gaban mai amfani da ita, tana fitar da ɗan ƙaramin girgiza tare da sautin faɗakarwa, domin bai wa mutum damar canza hanya kafin ya ci karo da abin.

Idan kuma ta gano rami ko wani wuri da ƙasa ta yi zurfi kwatsam, na’urar tana fitar da sauti mai ƙarfi kuma mai tsawo domin sanar da mai amfani da ita cewa akwai babban haɗari a gabansa.

Kara karanta wannan

Shin da gaske Atiku zai sayar da bankin CBN idan ya zama shugaban kasa?

Idan sandar ta kusanci ruwa ko ya shiga cikinsa, tana fitar da ƙananan sauti guda uku cikin sauri, domin mai amfani da ita ya bambanta sauran abubuwan da ta ke ganowa.

Tsarin aika saƙon gaggawa

Baya ga taimaka wa masu nakasar gani wajen gano cikas, sandar tana da wajen da ake sanya katin SIM.

Mai amfani da ita zai iya danna makunnin SIM din idan yana buƙatar taimako, inda na’urar za ta aika saƙon SMS kai tsaye zuwa ga wanda aka yi wa rajista a matsayin mai kula da shi ko kuma lambar gaggawa.

Wannan tsari na iya bai wa masu nakasas gani damar neman taimako cikin sauri ba tare da buƙatar amfani da wata na’ura daban ba.

Kofar ABU Zariya
Kofar shiga jami'ar ABU da ke Zariya. Hoto: ABU Zaria
Source: Twitter

Shirin da daliban suke yi

Ɗaya daga cikin ɗaliban da ke gabatar da sandar ya bayyana cewa suna shirin ƙara wasu fasahohi a na’urar a nan gaba.

Daga cikin abubuwan da ake shirin ƙarawa akwai tsarin GPS da zai ba masu kula da mai amfani damar bin inda yake ta hanyar manhajar waya.

Sun kuma shirya ƙara tsarin lura da ƙarfin batirin sandar, domin na’urar ta iya aika faɗakarwa idan batirin ya kusa ƙarewa yayin da ake amfani da ita.

Kara karanta wannan

IPOB ta yi barazanar da za ta shafi zaben 2027 saboda Nnamdi Kanu

Ga bidiyon daliban a kasa:

Atiku ya yi wa dalibai alkawari

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake duba tsarin NELFUND tare da yafe bashin ɗalibai.

Rahoto ya nuna cewa babban hadimin Atiku na musamman kan sadarwa, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

A bayanin da ya yi, ya ce Atiku bai yi imanin cewa ya kamata ɗaliban Najeriya su fara rayuwarsu ta aiki da nauyin manyan basussukan karatu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng