An Samu Kasar da Ta Yanke Hulda da Iran ana tsaka da Yaki da Amurka

An Samu Kasar da Ta Yanke Hulda da Iran ana tsaka da Yaki da Amurka

  • Gwamnatin kasar Peru ta yanke hulɗar diflomasiyya da Iran, tana zargin gwamnatin Tehran da ƙara tsananta rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya
  • Peru ta kuma zargi Iran da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz da kuma hana masu binciken makamashin nukiliya aiki
  • Kasar ta ce matakin nata ya samo asali ne daga damuwa kan take haƙƙin ɗan Adam, tauye ’yancin yaɗa labarai da kuma ƙara tashin hankali a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lima – Gwamnatin Peru ta sanar da yanke hulɗar diflomasiyya da Iran a ranar Talata, tana zargin Tehran da ƙara tsananta rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, takaita jigilar kayayyaki ta mashigar Hormuz da kuma hana binciken makamashin nukiliya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Peru ta ce gwamnatin ƙasar ta yanke wannan shawara ne saboda damuwar da take da ita kan yadda demokradiyya da haƙƙin ɗan Adam ke ci gaba da tabarbarewa a Iran.

Kara karanta wannan

IPOB ta yi barazanar da za ta shafi zaben 2027 saboda Nnamdi Kanu

Masoud Pezeshkian da Keiko Fujimori
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a hagu da sjugabar Peru Keiko Fujimori a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Zargin da Peru ta yi wa Iran

Anadolu ta wallafa cewa kasar Peru ta ce ta lura da yadda Iran ke murƙushe zanga-zangar lumana, tauye ’yancin ’yan jarida, nuna bambanci ga mata da ’yan mata da kuma tsananta wa ’yan adawar siyasa.

Ta ce waɗannan abubuwa sun saba da ƙudurin Peru na kare demokradiyya, wadda ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ƙa’idojin manufofinta na ƙasashen waje.

Magana kan mashigar Hormuz

Gwamnatin Peru ta kuma ce takaita zirga-zirgar kasuwanci da Iran ta yi ta mashigar Hormuz tun daga watan Maris na 2026 ya saba wa ƙa’idar ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa.

Ta ce matakin ya shafi tsaron zirga-zirgar ruwa, kare rayukan mutane a teku da kuma muhalli, tare da yin illa ga farashin makamashi da zaman lafiyar hanyoyin samar da kayayyaki a duniya.

Batun yaki a Gabas ta Tsakiya

Peru ta kuma zargi Iran da ƙarfafa tashin hankali da kuma ƙara tsananta rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya da ke cigaba da jawo matsaloli.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan hukumar EFCC 40 sun jawo wa kansu matsala a wurin aiki

Mojtaba Khamenei a Iran
Jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran International ta rahoto gwamnatin ta ce tana kuma yin Allah-wadai da abin da ta kira hana Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) gudanar da aikinta.

Peru ta ce hana masu binciken hukumar shiga wuraren da ake buƙatar bincika na kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da cewa Iran ba ta ƙera makaman nukiliya.

Iran ta kai hari kan Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan wuraren da sojojin Amurka suke a Jordan, Kuwait, Iraq da Bahrain bayan sojojin Amurka sun sake kai mata hari.

Kungiyar Red Crescent ta Iran ta ce mutane huɗu, ciki har da wani yaro, sun mutu yayin da wasu sama da 50 suka jikkata bayan tarkacen makamin Amurka ya faɗa kan wani gida da ake gudanar da bikin aure a Sirik.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nunaa cewa sojojin Amurka sun ce suna sane da rahoton, amma sun jaddada cewa ba su taɓa kai hari kan fararen hula da gangan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng