Bidiyo: Yadda Messi Ya Rika Rusa Kuka bayan Gaza Cin Kofin Duniya na 2026

Bidiyo: Yadda Messi Ya Rika Rusa Kuka bayan Gaza Cin Kofin Duniya na 2026

  • Tauraron ɗan ƙallon duniya, Lionel Messi, ya fashe da kuka bayan ƙasar Argentina ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2026
  • Messi ya zubar da hawaye yayin da ake damƙa masa lambar yabo ta matsayi na biyu, abin da da yawa ke gani a matsayin bankwanarsa da ƙwallon ƙasa da ƙasa
  • Masoya da 'yan jarida a faɗin duniya sun yi juyayi tare da girmama gudunmowar da Messi ya bayar bayan kammala wasan ƙarshen mai cike da ban tausayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shahararren ɗan ƙwallon ƙafar nan na duniya, Lionel Messi, ya yi kuka bayan tawagarsa ta Argentina ta sha kaye a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na shekarar 2026 da aka gudanar a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

A karshe, Peter Obi ya bar boye boye, ya fadi dalilin daukar Kwankwaso mataimakinsa

Messi ya zauna a filin wasan bayan kammala karawar, yana kallon yadda 'yan wasan ƙasar Spain ke gudanar da bukukuwan lashe kofin.

Lionel Messi na kuka
Lokacin da Lionel Messi ya fashe da kuka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yahoo Sport ta wallafa cewa Bayan karɓar lambar yabo ta matsayi na biyu, kamarori sun ɗauki hoton Messi yana zubar da hawaye cike da ban tausayi.

Gasar ta 2026 ta zamanto ta shida da Messi ya halarta, inda ya kafa tarihin kasancewa ɗan wasa na farko da ya shiga wasan ƙarshe na Kofin Duniya guda uku.

Tuni rahotanni suka fara nuna cewa dan wasan na daf da sanar da murabus dinsa daga taka leda a matakin ƙasa.

Martanin jama'a ga Messi

Kokarin da Messi ya yi a gasar sun sa mutane da dama bayyana ra'ayoyinsu. Tawagar ƙwallon ƙafa ta Argentina ta fitar da sanarwa tana cewa:

"Muna tare da kai, Kyaftin. Ka sanya mu farin ciki mafi girma a rayuwarmu. Mungode da sadaukarwa da kuma komai har zuwa daƙiƙa ta ƙarshe. Muna ƙaunarka har kullum, Leo!"

Ɗan jarida Henry Winter shima ya rubuta cewa:

"Gani Lionel Messi yana kuka abin ban tausayi ne kwarai. Shin yana tunanin rashin nasarar ne ko kuwa ƙarshen wasan shi na ƙasa da ƙasa? Ya kawo farin ciki ga duniyar ƙwallon ƙafa."

Kara karanta wannan

Shahararrun 'yan wasa 4 da ba su taɓa lashe Kofin Duniya ba a rayuwarsu

Shima ɗan jarida Roy Nemer cewa ya yi:

"Lionel Messi yana kuka. Dole ne mutum ya tunanin cewa wannan ne ƙarshen wasansa da Argentina. Shekaru 20 masu ban mamaki a tawagar ƙasar shi. Mungode da duk wani abin tunawa da ka bar mana."
Lionel Messi da Lamine Yamal
Lamine Yamal ya rungumi Lionel Messi bayan doke su. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Fox News ta wallafa bidoyon da Messi ya yi kuka a X:

Spain ta doke Argentina

A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙasar Spain ce ta zama zakaran gasar Kofin Duniya na FIFA na 2026 bayan ta doke zakarun baya, Argentina, da ci 1-0 bayan an ƙara ƙarin lokaci a wasan ƙarshe.

Ɗan wasan da aka sanya daga baya, Ferran Torres, ne ya zama jarumi ta hanyar jefa ƙwallon da ta tabbatar da nasarar Spain a sashe na biyu na ƙarin lokaci.

Golan Argentina, Emiliano Martínez, ya shafe lokaci da dama yana kare ragarsa daga ƙwallaye masu hatsari, amma abubuwa sun ƙara rikice wa Argentina a ƙarin lokaci da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng