Mbappe, Rodri da ‘Yan Wasan da Suka Lashe Kyauta a Gasar Kofin Kwallon Duniya

Mbappe, Rodri da ‘Yan Wasan da Suka Lashe Kyauta a Gasar Kofin Kwallon Duniya

  • Sifen ta lashe kofin duniya na shekarar 2026 bayan ta doke Argentina da ci 1-0 a wasan karshe da aka buga
  • Rodri ne gwarzon ‘dan kwallon gasar, shi kuma Kylian Mbappé da ya leka raga sau 10 ya fi kowa cin kwallaye
  • Kasar Sifen ta kafa tarihin zama tawagar farko da ta lashe kofin duniya yayin da aka zura mata kwallo guda rak

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

New York - Kasar Sifen ta yi nasarar lashe gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a wasan da aka buga ranar Lahadi, 19 ga Yuli 2026.

‘Yan wasan Sifen sun doke kasar Argentina da ci 1-0 a wasan karshe. Lionel Messi ya jagoranci kasarsa a filin New York a New Jersey.

Mbappe
'Dan wasan Faransa, Kylian Mbappe ya doke tarihin Lionel Messi Hoto: Sarah Stier - FIFA
Source: Getty Images

Kyaututtuka daga gasar cin kofin kwallon duniya

Bayanan da aka samu daga shafin FIFA mai kula da harkokin kwallon kafa sun tabbatar da ‘yan wasan da suka samu kyaututtuka.

Kara karanta wannan

Mbappe ya zarce Messi, ya kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya

‘Dan wasan tsakiyan Sifen, Rodri ya zama gwarzon ‘dan kwallo a gasar da aka yi makonni ana buga wa a Amurka, Canada da Mexico.

Tsohon abokinsa a Manchester City, Ikay Gundogan ya ji dadin wannan labari, ya taya Rodri murna da daren nan a shafinsa na X.

Ikay Gundogan da yake taya Rodri murna ya ce shakka babu ya cancanci wannan kyauta.

'Yan kwallon Sifen sun tashi da kyaututtuka

Unai Simón wanda kwallo guda kurum aka zura masa a raga a gasar shi ne gwarzon gola, ya shafe mintuna 350 ba a ci shi ba.

Kasar Netherlands ta ciri tuta wajen zama kasar da ta fi kowa bin ka’idoji da dokokin kwallo, FIFA ta sanar da haka a dandalin X.

Haka kuma hukumar ta sanar a X cewa a masu kananan shekaru, wanda ya fi kowa kokarin a gasar na 2026 shi ne Pau Cubarsi na Barcelona.

Kylian Mbappé ya fi kowa kwallaye a gasar 2026

‘Dan wasan gaba kuma kyaftin na kasar Faransa, Kylian Mbappé ya tabbata ‘dan kwallon da ya fi kowa kwallaye, ya ci kwallo sau 10.

Kara karanta wannan

Shahararrun 'yan wasa 4 da ba su taɓa lashe Kofin Duniya ba a rayuwarsu

Kylian Mbappé mai kwallaye 10 ya kafa tarihin zama ‘dan wasan kwallon kafa na farko da ya samu wannan kyauta sau biyu a jere.

Kuma shi ne dan wasa mafi yawan kwallaye a tarihin gasar kofin duniya na maza da kwallaye 22 a cewar wani rahoton Punch.

Lionel Messi yana bayan shi a gasar 2026 da kwallaye takwas sai Erling Haaland da ya ci bakwai.

Na uku a jerin shi ne Jude Bellinghman wanda ya ci kwallonsa na bakwai a wasan zama na uku da Ingila ta buga da Faransa.

Harry Kane da Osman Dembele suna da kwallaye shida. Sky Sports ta ce a jerin akwai Mikel Oyarzabal da ya zura biyar.

'Yan wasa da kasashen da suka samu kyaututtuka

1. Zakaru - Sifen

2. Masu bi masu (na 2) - Argentina

3. Na uku - Ingila

4. Na hudu - Faransa

5. Gwarzon ‘dan kwallo - Rodri

6. ‘Dan wasa mafi kwallaye - Kylian Mbappe

7. Gwarzon gola - Unai Simon

8. Yaro mai tasowa - Pau Cubars

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta garzaya kotu bayan kuskuren tura sama da N5m wani asusu

9. Masu bin doka da gaskiya - Netherlands

Yadda Sifen ta doke Argentina a wasan karshe

Legit Hausa ta kawo maku labari dalla-dalla a wasan karshe da Sifen ta lashe kofin duniya a karo na biyu a tarihinta bayan ta doke Argentina da ci 1-0.

Ferran Torres ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Sifen nasara a minti na 106, jim kaɗan bayan an dawo daga hutun ƙarin lokaci a birnin New York a Amurka.

Lionel Messi bai iya tabuka komai ba da 'yan wasa tara domin an kori ɗan wasan tsakiyar Argentina, Enzo Fernández, bayan ya karɓi katin gargadi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng