"Daidai Yake da Kofin Duniya"; Abin da Ronaldo Ya Fada bayan Rashin Nasarar Portugal
- Portugal wadda Cristiano Ronaldo ke jagoranra ta yi rashin nasara a hannun Spain a zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya
- Rashin nasarar ta kawo karshen kasancewar Cristiano Ronaldo a gasar cin kofin duniya wadda ya dade yana da burin lashewa
- Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa yana kofin da ya taba lashewa wanda a wajensa darajarsa tana daidai da ta kofin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Texas, Amurka - Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya yi magana kan rashin nasarar da suka yi a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa nasarar da ya samu a gasar Euro 2016 tare da Portugal tana da daraja iri daya a gare shi da kofin duniya.

Source: Getty Images
An kori Ronaldo a kofin duniya
Ya bayyana hakan ne da yake yin waiwaye kan karshen zuwansa gasar cin kofin duniya biyo bayan ficewa Portugal ta yi a zagaye 16 a hannun Spain a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026, cewar jaridar La Gazetta Dello Sport.
Spain ta doke Portugal da ci 1-0 a Arlington, Texas, albarkacin kwallon da dan wasa Mikel Merino ya zura a daidai lokacin da aka kara bayan cinye mintuna 90 babu ci.
Lamarin da ya kawo karshen gasar kofin duniya ta shida ta Ronaldo, kuma ta karshe kamar yadda shi da kansa ya bayyana.
Me Ronaldo ya ce bayan korar Portugal
Yayin da yake magana da manema labarai bayan kammala wasan, Ronaldo ya ce kofin nahiyar Turai da ya lashe tare da Portugal shekaru 10 da suka gabata yana da matukar muhimmanci a gare shi kamar kofin duniya.
“Na lashe gasar Euro 2016 kuma a gare ni tana da matsayi guda da kofin duniya. Wannan zai kasance har abada. Gobe wata sabuwar rana ce, kuma za mu ci gaba."
- Cristiano Ronaldo
Ronaldo ya ce bai da nadama
Ya bayyana cewa ba ya da wata nadama kan yadda gasarsa ta karshe ta kofin duniya ta kare, inda ya karkata akalar maganarsa maimakon haka zuwa ga jimillar kofunan da ya lashe tare da Portugal, rahoton The Mirror ya tabbatar da hakan.
“Zan tashi gobe da safe da irin yanayin da nake ciki a yau. Na yi iya kokarina. Na lashe kofuna uku tare da Portugal, kafin ni babu ko kofi guda. Zan iya kasancewa cikin farin ciki kawai."
- Cristiano Ronaldo

Source: Getty Images
Ronaldo ya gama zuwa kofin duniya
Ronaldo, wanda ya bayyana kafin wasan cewa wannan shi ne zai kasance zuwansa na karshe a kofin duniya, ya tabbatar da cewa ba zai sake zuwa gasar ba, kodayake bai fito fili ya yanke hukuncin daina buga wa kasarsa wasa gaba daya ba.
“Eh wannan shi ne kofin duniyata na karshe, amma yanzu zan samu lokacin yin tunani, na zauna da iyalina kuma rayuwa za ta ci gaba."
- Cristiano Ronaldo
Ronaldo ya yi bismillah
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan wasan gaba na Portugal, Criatiano Ronaldo, ya dauki hankula a gasar cin kofin duniya.
Yayin da Cristiano Ronaldo ke shirin bugun fenariti a wasan zagaye na 32 tsakanin Portugal da Croatia, an nuna shi kamar yana furta wasu kalmomi a hankali.
Kyamarorin da suka dauki dan wasan sun nuna cewa Ronaldo ya ce "Bismillah", yayin buga kwallo, wato kalmar Larabci mai nufin "Da sunan Allah."
Asali: Legit.ng

