Yadda Dan Wasan Kwallon Arsenal, Bukayo Saka, Ya Canjawa Yara Kusan 120 Rayuwa a Kano

Yadda Dan Wasan Kwallon Arsenal, Bukayo Saka, Ya Canjawa Yara Kusan 120 Rayuwa a Kano

  • Da yawa-yawan yan wasa dai musamman a Afrika Suna taimakawa inda suka fito dan ganin basu manta da asalinsu ba
  • Sadio Mane ya taimakawa kauyansu da ya fito ta hanyar gina masallaci, asibiti da kuma kai musu turken sadarwar 5G
  • Ahmed Musa ya kasance yana wannan irin taimakon musamman a azumin watan ramda ga wanda suka kasance masu karafin karfi

Dan wasan gefe na Arsenal, Bukayo Saka ya dauki nauyin ayyukan kula da lafiyar yara kusan 120 a jihar Kano. BigShoe kungiyar agaji da ta yi hadin gwiwa da Saka don taimaka wa yara matalauta da ayyukan kiwon lafiya, ta sanar da daukar nauyin a cikin wani sakon da ta wallafa a Twitter a ranar Alhamis.

Bukuyo saka
Yadda Dan Wasan Kwallon Kafa Ya Canjawa Yara Kusan 120 Rayuwa a Nigeria hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Kungiyar ta bayyana cewa an yi wa yaran aikin tiyata a babban asibitin kwararru da ke Kano.

Kara karanta wannan

2023: Ku Yi Hattara Da Peter Obi, Kungiyar Matasan Kirista Ta Aike Da Sako Mai Karfi Ga Yan Najeriya

“Muna alfahari da sanar dan uwanmu na BigShoe: @BukayoSaka87 A gabanin gasar cin kofin duniya ta 2022 kan mun rufe aikin tiyata 120 na yara a Kano, Najeriya. Babban godiya ga likitoci da tawagar Asibitin kwararru na Firimiya, ”.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A nasa jawabin, Saka ya ce a ko da yaushe yana farin cikin taimaka wa yaran da ke fuskantar kalubale su cimma burinsu.
"A gare ni, kowane yaro yana da dama iri ɗaya don cimma burinsu kuma idan da gaske zan iya yin wani abu don taimakawa, yana da mahimmanci a gare ni in yi hakan," in ji shi.
"Yana sa ni farin ciki sosai, musamman idan na ga yara suna farin ciki, iyayen suna farin ciki."
Duk da cewa ya zabi wakilcin Ingila a kan Najeriya, dan wasan mai shekaru 19 ya amince cewa yana jin alaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Kungiyar Miyetti Allah tayi watsi da Atiku, tace tana bayan Tinubu/Shettima

Ya kuma yaba BigShoe don tabbatar da aikin da gaskiya

Na ji albarkar kasancewa a matsayin da zan iya ba da gudummawa don sauƙaƙa rayuwar yara da kyautatawa ta hanyar wannan tiyatar."
"Har yanzu ina jin alaka da Najeriya sosai. A gare ni, yana da matukar mahimmanci in yi amfani da iyawata don samun tasiri mai kyau a inda zan iya kuma dole ne in faɗi babban godiya ga dukan ƙungiyar BigShoe don yin hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel