Bayan Shekaru 22 ba tare da Shinshina Kofin ba, Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya
- Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta Birtaniya ta kafa tarihi a gasar firimiya ta bana da ake bugawa ta shekarar 2025/2026
- Arsenal ta yi kokari sosai, ta samu ta lashe kofin gasar Firimiya ta kasar karo na farko cikin shekara 22 da suka gabata
- Hakan na zuwa ne bayan Manchester City ta yi kunnen doki da Bournemouth ranar Talata 19 ga watan Mayun 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, UK - Kungiyar kwalln kafa ta Arsenal da kocinta, Mikel Arteta sun kafa tarihi a gasar firimiya da ake yi a kasar Birtaniya.
Kungiyar Arsenal ta zama zakarar gasar Firimiya ta Birtaniya ta kakar 2025/2026 wanda hakan ya biyo bayan shafe shekaru 22 ba tare da lashe gasar ba.

Source: Getty Images
Dan jarida masanin harkokin wasanni, Fabrizio Romano ya tabbatar da haka a Facebook a yau Talata 19 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
"Na kira shugaban APC," Murray Bruce ya yi fatali da rahoton hana shi takarar sanata
Yadda wasan Manchester City ya ba Arsenal nasara
Wannan nasara ta Arsenal ta biyo bayan wasan Manchester City da ta tashi kunnen doki 1-1 da Bournemouth ranar Talata.
Nasarar ta tabbatar da cewa Arsenal za ta karbi kofin daga hannun Liverpool bayan ta samu tazarar maki biyar kafin wasan karshe na kakar bana.
Za a karrama kungiyar ta Arewacin London a filin wasa na Selhurst Park bayan wasansa da Crystal Palace a ranar Lahadi mai zuwa.
Arsenal ta kasance kungiyar da ta fi kowacce bajinta a gasar bana duk da cewa Manchester City ta dawo da karfinta daga baya.
Kocin kungiyar, Mikel Arteta ya lashe kofin gasar na farko a matsayinsa na mai horaswa bayan ya jagoranci kungiyar zuwa ga nasarar mai tarihi.

Source: Getty Images
Shekarun da Arsenal ta shafe ba firimiya
Wannan shi ne kofin Firimiya na farko da Arsenal ta lashe cikin shekara 22 tun bayan da yan wasanta suka yi bajinta ba tare da rashin nasara ba a 2004.

Kara karanta wannan
Kotu ta yanke wa Halima Umar hukunci bayan kama ta da makamai masu hadari a Filato
Kungiyar ta kafa tarihin cin kwallaye 19 daga bugun kusurwa, inda ta karya tsohon tarihin kwallaye 16 da aka taba kafawa a baya.
Arsenal ta kuma samu nasarori 28 a kakar bana, wanda ya zarce yawan nasarorin da wadancan yan wasan suka samu a kakar 2003/2004.
Wannan ne babban kofi na biyu da Arteta ya lashe tare da Arsenal bayan kofin FA na 2020 da kuma 'Community Shield' guda biyu.
Kungiyar yanzu na da damar kammala kakar bana cikin nasara da kafa tarihi idan ta doke PSG a wasan karshe na Zakarun Turai a Budapest.
'Dalilin da ya sa Dangote bai sayi Arsenal ba'
Mun ba ku labarin cewa hamshakin attajirin da babu kamarsa a nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya yi tsokaci kan batun yunkurin sayan kungiyar Arsenal a shekarun baya.
Aliko Dangote ya bayyana cewa wani lissafi ya yi a wancan lokacin, wanda hakan ya sanya ya yanke shawarar fasa mallakar kungiyar kwallon kafar.
Hamshakin attajirin ya bayyana cewa ya auna ya ga abin da ya fi muhimmanci tsakanin sayan kungiyar Arsenal da kammala aikin matatar man sa da ke Lagos.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng