AFCON 2025: CAF Ta Saki Jadawalin Wasanni, Super Eagles Za Ta Kara da Kasashe 3

AFCON 2025: CAF Ta Saki Jadawalin Wasanni, Super Eagles Za Ta Kara da Kasashe 3

Morocco - Hukumar CAP ta tabbatar da jadawalin wasannin rukunai na gasar cin Kofin Nahiyar Afrika ta 2025 (21 ga Disamba 2025 – 18 ga Janairu 2026) a Morocco.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yanzu kasashe 24 sun san abokan karawarsu a taron fitar da jadawalin da aka gudanar a Rabat ranar Litinin (27 ga Janairu), ciki har da Cote D'Ivoire mai rike da kofin.

CAP ta fitar da jadawalin wasannin gasar cin kofin Nahiyar Afrika (AFCON 2025)
Najeriya za ta fafata da kasashe 3 a rukunin wasannin cin kofin AFCON 2025. Hoto: @CAF_Online
Asali: Getty Images

Ƙasashen sun samu zuwa wannan matakin ne ta hanyar fafatawa a zagaye na farko na cancantar shiga gasar ta hukumar CAF, inji rahoton shafin Olympics.

CAP ta fitar da jadawalin wasannin AFCON 2025

An raba ƙasashe 48 zuwa rukunoni 12, kowanne rukuni na da ƙasashe huɗu da suka fafata a gida da waje cikin wasanni shida.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA ta yi babban kamu, dillalan hodar iblis sun shiga hannu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan ƙasashe biyu a kowanne rukunin sun samu tsallake wasannin sharar fage, tare da shiga jadawalin babbar gasar cin kofin AFCON ta 2025.

Za a gudanar da gasar AFCON 2025 a cikin garuruwa shida a tsawon makonni huɗu, a karshe dai, ƙasa ɗaya ce za ta iya zama zakarar gasar.

Ga dukkan muhimman bayanai game da gasar cin Kofin Nahiyar Afrika ta 2025.

AFCON 2025 - Jadawalin wasannin rukunoni

Rukunin 'A'Rukunin 'B'Rukunin 'C'Rukunin 'D'Rukunin 'E'Rukunin 'F'
Morocc0EgyptNigeriaSenegalAlgeria Cote D'Ivoire
MaliSouth AfricaTunisia DR CongoBurkina FasoCameroon
ZambiaAngolaUgandaBeninEquatorial GuineaGabon
ComorosZimbabweTanzania BotswanaSudanMozambique

AFCON 2025 - Yadda tsarin gasar yake

Za a fara AFCON 2025 a ranar 21 ga Disamba 2025, inda Morocco za ta kara da Comoros a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a daren Juma'a, mutanen gari sun masu tara tara, an rasa rai

Kungiyoyi 24 aka rarraba su zuwa rukuni shida, kowanne rukuni na dauke da kungiyoyi hudu. Za su buga zagaye na farko, inda kowace kungiya za ta kara da sauran uku.

Kungiyoyi biyu daga kowanne rukuni da suka yi nasara za su samu gurbin zuwa matakin gaba. Daga cikin kungiyoyi shida da suka zo na uku, guda hudu za su cike guraben zagaye na 16.

Da an shiga zagaye na 16, za a koma tsarin korar duk kungiyar da ta yi rashin nasara har zuwa wasan karshe na AFCON 2025, wanda za a buga ranar 18 ga Janairun 2026.

Yayin da aka tabbatar da jadawalin wasannin, rahoto ya nuna cewa ana iya sauya lokutan fara wasanni.

AFCON 2025 - Filayen da za a buga wasanni

Za a gudanar da AFCON 2025 a Morocco a manyan filayen wasanni guda shida da ke biranen ƙasar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi galaba a kan manyan 'yan ta'adda a Zamfara

Ga jerin filayen:

1. Prince Moulay Abdellah, da ke garin Rabat

2. Stade Mohamed V, da ke garin Casablanca

3. Stade de Marrakech, da ke garin Marrakech

4. Stade Adrar, da ke garin Agadir

5. Stade Ibn Batouta, da ke garin Tangier

6. Stade Fez, da ke garin Fez

Waɗannan filayen za su karɓi bakuncin dukkanin wasannin gasar daga zagayen farko har zuwa wasan ƙarshe na ranar 18 Janairun 2026.

AFCON 2025: Jadawalin wasanni, rana da lokaci

Ga cikakken jadawalin wasannin AFCON 2025 a rukunin farko, tare da lokacin da za a buga kowanne wasa. Duk lokacin yana a tsarin lokacin WAT.

Lahadi 21 Disamba 2025

Rukunin A: Morocco vs Comoros (Rabat 1, karfe 8:00 na dare)

Litinin 22 Disamba 2025

Rukunin A: Mali vs Zambia (Rabat 2, karfe 3:30 na rana)

Rukunin B: Egypt vs Zimbabwe (Agadir, karfe 6:00 na yamma)

Kara karanta wannan

Jami'an gwamnatin El Rufa'i sun goyi bayansa, an zargi Uba Sani da bita da kullin siyasa

Rukunin B: South Africa vs Angola (Marrakech, karfe 8:30 na dare)

Talata 23 Disamba 2025

Rukunin C: Nigeria vs Tanzania (Fes, karfe 1:00 na rana)

Rukunin C: Tunisia vs Uganda (Rabat 4, karfe 3:30 na rana)

Rukunin D: Senegal vs Botswana (Tangier, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin D: DR Congo vs Benin (Rabat 3, karfe 8:30 na dare)

Laraba 24 Disamba 2025

Rukunin E: Algeria vs Sudan (Rabat 2, karfe 1:00 na rana)

Rukunin E: Burkina Faso vs Equatorial Guinea (Casablanca, karfe 3:30 na rana)

Rukunin F: Cote D'Ivoire vs Mozambique (Marrakech, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin F: Cameroon vs Gabon (Agadir, karfe 8:30 na dare)

Jumma’a 26 Disamba 2025

Rukunin A: Morocco vs Mali (Rabat 1, karfe 1:00 na rana)

Rukunin A: Zambia vs Comoros (Casablanca, karfe 3:30 na rana)

Rukunin B: Egypt vs South Africa (Agadir, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin B: Angola vs Zimbabwe (Marrakech, karfe 8:30 na dare)

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: An kama 'yan kasashen waje 165 da shirin kulla makirci a Najeriya

Asabar 27 Disamba 2025

Rukunin C: Nigeria vs Tunisia (Fes, karfe 1:00 na rana)

Rukunin C: Uganda vs Tanzania (Rabat 3, karfe 3:30 na rana)

Rukunin D: Senegal vs DR Congo (Tangier, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin D: Benin vs Botswana (Rabat 4, karfe 8:30 na dare)

Lahadi 28 Disamba 2025

Rukunin E: Algeria vs Burkina Faso (Rabat 2, karfe 1:00 na rana)

Rukunin E: Equatorial Guinea vs Sudan (Casablanca, karfe 3:30 na rana)

Rukunin F: Cote D'Ivoire vs Cameroon (Marrakech, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin F: Gabon vs Mozambique (Agadir, karfe 8:30 na dare)

Litinin 29 Disamba 2025

Rukunin A: Zambia vs Morocco (Rabat 1, karfe 6:30 na yamma)

Rukunin A: Comoros vs Mali (Casablanca, karfe 6:30 na yamma)

Rukunin B: Angola vs Egypt (Agadir, karfe 8:30 na dare)

Rukunin B: Zimbabwe vs South Africa (Marrakech, karfe 8:30 na dare)

Talata 30 Disamba 2025

Rukunin C: Uganda vs Nigeria (Fes, karfe 6:00 na yamma)

Kara karanta wannan

Tankoki 2 makare da fetur sun fashe a wani gidan mai a Adamawa, gobara ta tashi

Rukunin C: Tanzania vs Tunisia (Rabat 4, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin D: Benin vs Senegal (Tangier, karfe 8:30 na dare)

Rukunin D: Botswana vs DR Congo (Rabat 3, karfe 8:30 na dare)

Laraba 31 Disamba 2025

Rukunin E: Equatorial Guinea vs Algeria (Rabat 2, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin E: Sudan vs Burkina Faso (Casablanca, karfe 6:00 na yamma)

Rukunin F: Gabon vs Cote D'Ivoire (Marrakech, karfe 8:30 na dare)

Rukunin F: Mozambique vs Cameroon (Agadir, karfe 8:30 na dare)

'Najeriya na bukatar jajurcewa' - Saminu

Saminu Abdullahi Namunaye, mai sharhi kan wasanni daga Bauchi, ya yi tsokaci kan rukunin 'E' da Najeriya take ciki a AFCON 2025.

“Za a fafata sosai a rukunin C da Najeriya ke ciki, amma ina da yakinin cewa Super Eagles za su iya samun nasara,” inji Saminu.

Ya ce:

“Fafatawa da samun nasara kan kasashe masu ƙarfi kamar Mali na bukatar kwarewar 'yan wasan Najeriya, kuma dole ne mu magance matsalolin da aka samu a 2024.”

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka kashe jami'an 'yan sanda, NSCDC, NIS da sojoji 326 a Najeriya

“Samun nasara a wasan farko yana da matuƙar muhimmanci wajen sanyan kwarin gwiwa a 'yan wasa, wanda zai yi tasiri a kansu a wasannin gasar gaba ɗaya."

Saminu ya ce 'yan Najeriya da magoya bayan tawagar Super Eagles su shirya ma gasar AFCON ta bana, yayin da ya yi kira ga hukumar Super Eagles ta fara shiri tun wuri.

Ivory Coast ta lashe kofin AFCON 2024

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ranar 11 ga Fabrairu, 2024, Côte d'Ivoire ta doke Najeriya 2-1 a wasan karshe na AFCON a filin wasa na Abidjan.

William Troost-Ekong ya fara cin kwallo, Franck Kessié ya farke, sannan Sébastien Haller ya ci kwallon da ta ba Côte d'Ivoire nasara a minti na 81.

Côte d'Ivoire ta lashe kofin AFCON karo na uku a tarihi, yayin da Najeriya ta kammala gasar a matsayi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.