Jami'an Gwamnatin El Rufa'i Sun Goyi Bayansa, An Zargi Uba Sani da Bita da Kullin Siyasa
- Tsoffin mambobin Majalisar Zartarwar Jihar Kaduna sun bayyana zargin cin hanci da rashawa a kansu a matsayin bita da kulli
- Sun ƙi yarda da rahoton Majalisar Kaduna wanda ya ce an rasa Naira biliyan 423 a ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai
- Tsofaffin jami’an sun zargi gwamnatin Uba Sani da ɗaukar ayyukan El-Rufai da aka ƙaddamar a lokacin mulkinsa kamar na ta
- Sun bayyana cewa gwamnatin Uba na ƙoƙarin hana sakin makusantan El-Rufai da ta kama ba bisa ka'ida ba bisa zargin bogi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsofaffin ƴan Majalisar Zartarwar Jihar Kaduna (2015-2023) sun musanta zargin cin hanci da rashawa da ake musu da gwamnatin Nasir El Rufa’i.
Sun bayyana zargin da ake wa gwamnatinsu a matsayin wani yunkuri na siyasa da gwamnatin Uba ke yi masu, yayin da su ka yaba da shugabancin El-Rufai a lokacin da yake ofis.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsofaffin jami’an sun ƙi yarda da rahoton Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, wanda ke cewa an rasa Naira biliyan 423 a ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun ce wannan zargi karya ne kuma ana yin haka ne domin lalata siyasar tsohon gwamnan da da kuma cimma manufar siyasa.
An musanta zargin da ake yi wa El Rufa’i
Premium Times ta wallafa cewa tsofaffin jami’an sun dage wajen musanta zargin majalisar dokokin Kaduna na watan Yuni da Yulin 2024, suna nuna cewa zargin ba shi da tushe.
Sun ce da yawa daga cikin basussukan da aka lissafa a cikin rahoton ba a dauke su a ƙarƙashin shugabancinsu.
Wasu basussukan, a cewarsu, an fito da su fiye da sau ɗaya, da kuma zargin an sa basussukan hanyoyin jirgin ƙasa wanda ba a taɓa ɗauka ba a cikin rahoton.
Ana zargin gwamna da bibiyar makusantan El-Rufai

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun yi dirar mikiya kan 'yan ta'adda, sun hallaka miyagu masu yawa
Bayan zarginsa da rashawa, tsofaffin jami’an sun ce gwamnatin Uba Sani na ƙoƙarin takura wa makusanta Nasir El Rufa’i.
Sun kawo misalin Bashir Saidu, wanda ake zargin ‘sace’ shi a Kaduna ranar 31 ga Disamba, 2024, kuma har yanzu yana daure a kurkuku duk da an ba shi beli.
"Bi-ta-da-kulli ya ke masa," Masoyan El-Rufa’i
Tsofaffin jami’an sun ce ainihin manufar wannan zargi shi ne ɓata sunan El-Rufai da kuma kawo masa cikas a harkokin siyasarsa.
Sun ce tun da bai tabbatar da zargin Naira biliyan 423 ba, gwamnatin na kokarin amfani da kafafen yada labarai da kuma shigar da ƙorafe-ƙorafe na laifi kan tsofaffin jami’an domin jingina masa laifi.
An shawarci El Rufa'i ya bar siyasa
A wani labarin, kun ji cewa rikicin siyasa tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da gwamnan yanzu, Uba Sani, ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
El-Rufai ya bayyana cewa yanzu ya fahimci dalilin da ya sa Uba Sani ke goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya alakanta da kudin da aka ba Kaduna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng