Barazanar Tsaro: An Kama 'Yan Kasashen Waje 165 da Shirin Kulla Makirci a Najeriya
- 'Yan sanda sun kama mutane 165 da suka fito daga ƙasashen Burkina Faso, Mali, Ivory Coast, Benin, da Nijar ba tare da takardun izinin zama ba
- An gano su ne a cikin gini mai dakuna uku a unguwar Kuwait da ke Birnin Kebbi, inda ake zargin suna da hannu a wata harkar zamba
- Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin sun bayyana damuwa kan barazanar tsaro da irin waɗannan baƙin haure ke haifarwa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama mutane 165 da ba su da takardun izinin zama a Najeriya, daga ƙasashen Burkina Faso, Ivory Coast, Benin Republic, Mali da Nijar.
An kama su ne a wani gida mai dakuna uku da ke unguwar Kuwait a Birnin Kebbi, biyo bayan rahoton sirri da ya kai ga gano su.

Asali: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa kakakin ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa jami’an binciken manyan laifuffuka na rundunar (SCID) ne suka kama su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasashen da bakin suka fito
'Yan sanda sun bayyana cewa an kama bakin hauren ne da suka fito daga kasashe da suka hada da:
- Burkina Faso 35
- Ivory Coast 110
- Jamhuriyar Benin 11
- Jamhuriyar Nijar 5
- Mali 4
Zargin yin harkar zambar Qnet
CSP Abubakar ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka kama suna zaune a Najeriya ba tare da takardun izinin zama na doka ba.
Ana zargin su da hannu a wata harkar zamba mai suna Qnet, wanda ake amfani da ita wajen yaudarar mutane da alkawarin samun riba mai yawa idan aka saka hannun jari.
"Bayan kammala bincike, an mika su ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya (NIS) reshen jihar Kebbi domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace,"

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki
- CSP Abubakar
Alakar bakin haure da tsaro a Kebbi
Mazauna unguwar Kuwait da ke Birnin Kebbi sun bayyana damuwa kan kasancewar waɗannan baƙin haure a cikin unguwar ba tare da sanin takamaiman abin da suke yi ba.
Daya daga cikin mazauna yankin mai suna Adamu Augie ya ce:
"Mun sha ganin waɗannan mutanen na shiga da fita daga gidan nan tun watanni da suka wuce. Ba mu san abin da suke yi ba, amma a fili yake cewa ba 'yan Najeriya ba ne."
Augie ya ƙara da cewa kasancewar su a yankin ya sa wasu daga cikin mazauna unguwar suka kai rahoto ga ‘yan sanda saboda fargabar barazanar tsaro.
"A halin yanzu da ake fama da matsalolin tsaro a ƙasar nan, ba za mu iya yin sakaci ba,"
- Adamu Augie
Wani mazaunin yankin, Abdullahi Umar, ya tabbatar da cewa samamen da ‘yan sanda suka gudanar ya biyo bayan bayanan da mazauna yankin suka bayar.
Sojoji sun kama makamai a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kama wata mota dauke da tarin makamai a karamar hukumar Barikin Ladi na jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa an kama mutum daya daga cikin wadanda suka taho da motar yayin da sauran mutanen suka gudu bayan sojoji sun tunkare su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng