Hukumar NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Dillalan Hodar Iblis Sun Shiga Hannu
- Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi sun cafke dillalan hodar iblis a filayen jiragen sama
- Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke mutanen ne guda biyu da ake zargi da safarar hodar iblis a Port Harcourt da Legas
- Dukkanin waɗanda ake zargin sun kasayar da jimillar hodar iblis har ƙunshi 125 bayan sun shiga hannun jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta cafke wasu dillalan hodar iblis mutum biyu.
Hukumar NDLEA ta cafke mutanen ne a filayen jiragen sama na Port Harcourt da na Murtala Muhammed da ke Legas.

Asali: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafin X na hukumar a ranar Lahadi.
Wadanda ake zargi sun kasayar da hodar iblis
Mutanen biyun da aka kama sun fitar da jimillar ƙunshi 125 na hodar iblis daga cikinsu.
Femi Babafemi ya bayyana cewa ɗaya daga waɗanda ake zargin, Onyekwonike Elochuckwu Sylvanus, yana amfani da sunaye biyu domin kaucewa kamun jami'an tsaro.
Sylvanus, mai shekaru 30, an kama shi a filin jirgin sama na Port Harcourt a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2025, yana amfani da fasfo na ƙasar Sierra Leone da sunan Kargbo Mohamed Foday.
Jami'an na NDLEA sun cafke shi ne yayin da yake ƙoƙarin shiga Najeriya daga birnin Doha na ƙasar Qatar ta hanyar birnin Abuja.
"Bayan an yi masa binciken jiki, an gano cewa ya haɗiye miyagun ƙwayoyi. Bayan an sanya masa ido, ya fitar da ƙunshi 62 na hodar iblis mai nauyin 1.348kg."
- Femi Babafemi
Bincike ya gano cewa Sylvanus yana amfani da fasfo na Najeriya da Sierra Leone domin safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Thailand, Pakistan, Iran, da yammacin Afirka.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi tsaurin ido, sun yi garkuwa da Birgediya Janar Maharazu Tsiga
Ya amsa cewa ya shiga harkar safarar miyagun ƙwayoyi tun a shekarar 2017, bayan da kasuwancin sayar da kaya da takalma da yake yi ya rushe.
NDLEA ta cafke dillalin hodar iblis a Legas
Mutum na biyu, James Chinoso, mai shekaru 48, an kama shi ne a filin jirgin sama na Legas a ranar 1 ga watan Fabrairu, 2025, bayan dawowarsa daga ƙasar Madagascar ta jirgin Ethiopian Airlines.
"Bayan yi masa binciken jiki, an gano ya haɗiyr miyagun ƙwayoyi a cikinsa. Bayan an sanya masa ido, ya fitar da ƙunshi 63 na hodar iblis mai nauyin 909grm.
- Femi Babafemi.
Bincike ya nuna cewa Chinoso ya bar Legas zuwa Madagascar a ranar 26 ga watan Janairu, 2025, kuma ya dawo Najeriya mako guda bayan tafiyarsa.
Ya bayyana cewa ya shiga harkar safarar miyagun ƙwayoyi ne bayan da kasuwancin sayar da wayoyi da yake yi a ƙasar Liberia ya rushe.
NDLEA ta cafke dattijo a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), sun cafke wani dattijo mai dillancin tabar wiwi.
Jami'an na NDLEA sun cafke dattijon mai shekara 75 ne a ƙauyen Tumbau da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.
Asali: Legit.ng