Siyasar Najeriya
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyana yiwa fursunoni 115 afuwa biyo bayan nazari mai zurfi kan cunkoson da ke yawan faruwa a gidajen yarin kasa Najeriya.
Yayin da ya rage awanni 48 gabannin rantsar da sabon shugaban kasa a Najeriya, majalisar dattawan Najeriya ta shiga zaman gaggawa a zaurenta da ke birnin Abuja.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar zartaswan jiharsa gabanin ranar rantsarwa, ya ce za su amshu kyauta ta musamman.
Sanata Smart Adeyemi daga jihar Kogi, ya shawarci Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki mataki kan gwamnan CBN, Godwin Emefiele da sauran masu hannu a canjin kudi.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar zartarwan jiharsa, ya ce duk wanda ya masa laifi ya yafe masa, sannan kuma ya roki su yafe masa.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce kullum yana kirga ragowar ranakun da suka rage masa a ofis domin ya ƙosa ya mika ragamar mulki ga zababben shugaban ƙasa.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana cewa ya samu labarin yadda wasu daga cikin mambobin majalisarsa suka yaƙe shi a lokacin babban zaben 2023.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya tabbatar da cewa ba zai juya da baya ba, lauyoyin da ya haɗa zasu tabbatar da zaben 2023 damfara ne.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya sallami dukkan mambobin majalisar zartaswa ana saura kwana 4 gabanin sake rantsar da shi a zango na biyu.
Siyasar Najeriya
Samu kari