Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya Ya Tashi Zuwa 21.91% Yayin da Ake Fama da Karancin Naira

Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya Ya Tashi Zuwa 21.91% Yayin da Ake Fama da Karancin Naira

A cikin shekaru 17, ba a taba ganin hauhawar farashin kayayyaki da ya taba faruwa cikin watanni biyun nan ba

 • Rahoto ya bayyana jihohin Najeriya da hakan ya fi shafa, inda aka bayyana jihar Bauchi a sama, sai kuma Sokoto a kasan jerin
 • Wannan lamari ya sa babban bankin Najeriya zai zauna domin tabbatar da kawo mafita ga lamarin a cikin watan Maris

Ma'aunin farashi kayayyaki na CPI da ke auna hawa da saukan farashin kayayyaki ya bayyana yadda farashin kayayyaki ya karu a Najeriya zuwa 21.19% a watan Faburairun 2023.

A watan da ya gabata, farashin kayayyakin ya tsaya ne a kaso 21.82%, duk dai a fama da ake da karancin Naira a kasar, TheCable ta ruwaito.

Rahoton hauhawar farashin kayayyakin na kunshe ne cikin sabon rahoton CPI da aka hukumar kididdiga ta NBS ta fitar a ranar Laraba 15 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Pantami: An yi Yunkurin yi wa Najeriya Kutse Kusan Sau Miliyan 13 Lokacin Zaben 2023

Yadda kaya suka tashi a Najeriya
Allon da ke nuna yadda kaya suka tashi a Najeriya | Hoto: NBS
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan karin na zuwa ne a karo na biyu a jere a cikin shekarar, a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fama da kuncin karancin sabbin Naira.

Yadda lamarin ya shafi jihohin Najeriya

A watan Faburairu, NBS ta fitar da rahoton cewa, hauhawar farashi na shekara-shekara ya sama a jihohi kamar haka:

 1. Bauchi (24.59%)
 2. Rivers (24.40%)
 3. Ondo (24.27%)
 4. Sokoto (18.90%) Borno (18.94%)
 5. Cross River (19.62%)

A matakin wata-wata kuwa, an naqalto yadda lamarin ya kasance a watan Faburairun da ta shude kamar haka:

 1. Edo (2.76%)
 2. Ogun (2.64%)
 3. Yobe (2.36%)
 4. Bayelsa (0.74%)
 5. Borno (0.95%)
 6. Taraba (1.03%)

A halin da ake ciki a Najeriya, karancin takardun Naira na daya daga cikin abubuwan da ke ba 'yan kasar ciwon kai.

Bankuna za su fara ba da tsoffin kudi, amma da sharadi

A wani labarin, kunji yadda bankunan Najeriya suka bayyana ba da tsoffin takardun Naira a daidai lokacin da 'yan kasar ke cikin wani yanayi na matsi.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

A binciken da aka yi, wasu bankuna na ba da N20,000 ga kwastomomi a cikin banki, N10,000 kuma a bakin ATM.

Wadanda ba kwastomominsu ba kuwa kodai su gaza samun kudin, ko kuma a basu kudin da bai taka kara ya karya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel