Zaben 2023: Bayan Sarkin Musulmi Ya Saka Baki, Yan Takarar Gwamna Na NNPP Da SDP Sun Janye Wa APC A Nasarawa

Zaben 2023: Bayan Sarkin Musulmi Ya Saka Baki, Yan Takarar Gwamna Na NNPP Da SDP Sun Janye Wa APC A Nasarawa

  • Manyan yan takarar Gwamna na jam'iyyun SDP da NNPP sun janye takara a Jihar Nasarawa ana daf da shiga zabe
  • Hakan na zuwa ne bayan ziyarar tawagar sarkin musulmi, tare da rokon yan takara musulmi da su mara wa Abdullahi Sule na Jam'iyyar APC baya
  • Shima tsohon gwamnan Jihar, Tanko Al-Makura ya bukaci da yan jam'iyyar APC su hada kai don tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a zaben gwamnoni da za a gudanar ranar Asabar

Nasarawa - A shirye shiryen zaben gwamna da za a gudanar ranar Asabar, biyu daga cikin manyan yan takarar gwamna a Jihar Nasarawa sun janyewa Gwamna Abdullahi Sule, wanda ke neman tazarce a inuwar jam'iyyar APC, rahoton Guardian.

Wannan na zuwa biyo bayan ziyarar sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ll, zuwa Lafia a baya bayan nan.

Kara karanta wannan

Ana Daf Da Zabe, Makisa Sun Kai Wa Dan Takarar Gwamnan PDP Hari

Gwamna Abdullahi Sule
Yan takarar gwamna na NNPP da SDP sun mara wa Gwamna Sule baya a Nasarawa. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sarkin musulmin ya jagoranci wata tawaga mai karfi zuwa Lafia don rokar yan takarar gwamna Musulmi da su janyewa gwamna mai ci na jam'iyyar APC.

Sheikh Dahiru Bauchi, wanda ya wakilci sarkin musulmin ya roki dan takarar SDP, Mohammed Alfa-Nyass; da dan uwansa na jam'iyyar NNPP, Abdullahi Maidoya da su janye wa Sule a zaben gwamnan ranar Asabar.

Biyo bayan shigowar sarkin musulmi maganar, jam'iyyar SDP da NNPP, a wani taron manema labarai da suka yi a Lafia, jiya, sun janye takarar ga ''jam'iyyar da za su bayyana nan gaba.''

A wani rahoton, Sanata Tanko Al-Makura (na jam'iyyar APC, mai wakiltar Nasarawa ta kudu) ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar APC da su sake zabar Sule a zaben gwamnoni na ranar Asabar.

Sanatan ya yi kira ga yan jam'iyyar da su hada kai a zaben ranar Asabar don tabbatar da nasara.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Jam’iyyun Siyasa 4 Ke Shirin Maja Don Tsige Gwamnan APC a Wata Jihar Arewa

Gwamna Sule ya ce lokacin da aka gudanar da zaben shugaban kasa ake kuma ganin dan takarar Jam'iyyar Labour, Peter Obi ne zai lashe jihar, bai yadda ba sai kuma hasashen ya tabbata.

Ya kara da cewa:

''Sannan, akwai wani hasashen cewa zaben gwamnan Nasarawa tsakanin APC da PDP ne. Akwai bukatar mu hada kai muyi aiki tukuru idan muna bukatar yin nasara.''

Kwankwaso zai yi gadon farin jinin Buhari, A cewar Bashir El-Rufa'i

Dan Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, Bashir, ya yi hasashen cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023 shine zai gaji farin jinin Shugaba Muhammadu Buhari.

A cewar Bashir, duk wadanda ke yi wa Kwankwason dariya yanzu za su sha mamaki a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel