Kasar Amurka Ta Taya Tinubu Murnar Lashe Zabe, Ta Ba ’Yan Najeriya Sakon a Zauna Lafiya

Kasar Amurka Ta Taya Tinubu Murnar Lashe Zabe, Ta Ba ’Yan Najeriya Sakon a Zauna Lafiya

  • Kasar Amurka ta taya Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa da aka yi kwanan nan
  • Hakazalika, sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankali kana su karbi Tinubu hannu bibbiyu
  • Nasarar Bola Ahmad Tinubu ta tada hankalin ‘yan adawa, yanzu haka wasu suna kokarin tafiya kotu

Kasar Amurka - Kasar Amurka ta taya 'yan Najeriya da Bola Ahmad Tinubu murnar lashe zabe yayin da ta yi kira ga a kwantar da hankali bayan da ake ci gaba da cece-kuce kan nasararsa.

Kasar ta kuma bayyana cewa, ta fahimci akwai matsalolin da zaben ya zo da shi, amma ya kamata mutane su kwantar da hankali tare da taya Tinubu rikon kasar.

Wannan batu na Amurka na zuwa ne a ranar Laraba 15 ga watan Maris, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hangen nesa: Babban malami ya roki Buhari ya kori babban jami'in INEC saboda matsala 1

Amurka ta taya Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa
Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Tinubu ya lashe zabe, Amurka ta yi magana

An ayyana Tinubu ne a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a zaben 25 ga watan Faburairu bayan samun kuri’u sama da miliyan 8.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar kakakin kasar, Ned Price:

“Kasar Amurka na taya jama’ar Najeriya, zababben shugaban kasa Tinubu da dukkan shugabannin jam’iyyun siyasa murna.
“Wannan zabe mai cike da gasa yana nuna sabon lokaci ga ‘yan siyasan Najeriya da dimokradiyya.”

Akwai lam’a a zaben bana, inji Price

A bangare guda, Price ya bayyana yadda wasu ‘yan Najeriya ke nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben, inda ‘yan takarar adawa biyu suka bayyana tafiya kotu.

Ya kara da cewa:

“Mun fahimci cewa ‘yan Najeriya da dama da wasu jam’iyyun siyasa sun nuna damuwa game da yadda aka gudanar da zaben.
“’Yan Najeriya na da ‘yancin jin irin wannan yanayi kuma suna da damar tsammanin abin da suke so a zabe.”

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

Daga karshe, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su kauracewa tada hankali da cece-kuce a irin wannan yanayin.

Atiku da Obi za su tafi kotu, an ba su damar bincika kayan aikin zabe

A halin da ake ciki, an ba ‘yan jam’iyyar adawa, Peter Obi da Atiku Abubakar damar bincika kayan aikin zaben bana don tabbatar da inda aka samu matsala ko kuskure.

Hakazalika, Tinubu ya samu irin wannan damar don samun hanyar da zai kare kansa a kotun da za a shiga nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel