Dubban ‘Ya’yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa SDP a Jihar Katsina

Dubban ‘Ya’yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa SDP a Jihar Katsina

  • Yan Kwanaki kafin zaben gwamnoni, jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta yi babban kamu a jihar Kastina
  • Dubban mambobin babbar jam'iyyar adawa ta PDP sun sauya sheka zuwa SDP a jihar ta arewa
  • SDP ta ce tana samun karin magoya baya a kwanakin nan daga jam'iyyun siyasa daba-daban

Katsina - Akalla mambobin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) dubu arba'in da biyar ne suka fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Katsina, Channels TV ta rahoto.

Yayin da yake tarban masu sauya shekar a ranar Talata, 14 ga watan Maris, dan takarar gwamnan SDP a jihar, Ibrahim Zakari Talba, ya nuna farin cikinsa a kan ci gaban.

Wasu daga cikin masu sauya shekar
Dubban ‘Ya’yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa SDP a Jihar Katsina Hoto: Channels TV
Asali: UGC

SDP ta samu karbuwa a jihar Katsina, Ibrahim Zakari Talba

Ya ce sauya shekarsu ya nuna matakin karbuwar da jam'iyyar SDP ke samu daga mutane.

Kara karanta wannan

Sakataren PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Maida Martani Mai Zafi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Talba, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Arch. Ibrahim Suleiman, ya sanar da cewar SDP na ta tarban magoya baya daga jam'iyyun siyasa daban-daban wanda wasu daga cikinsu a boye ne yayin da sauran suka fito fili.

"Mun ba da tabbacin rike su don zama cikin tsarin.
"Talba ya kasance shugaba mai hangen nesa da kishin kasa da muke bukata wanda ke da kasar a zuciya."

Yawancin masu sauya shekar karkashin jagorancin Abubakar Sani da Sabi'u Dutsi, sun fito ne daga kungiyoyin Ladon Alkhairi da na kamfen din PDP Mafita, rahoton Opera News.

Zaben gwamnoni ya fi na shugaban kasa rikitarwa, NSA Monguno

A wani labari na daban, babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya magantu a kan zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

NSA Monguno ya ce zaben gwamnoni yana fin na shugaban kasa rikitarwa sosai saboda akwai banbanci a tsakanin zabukan biyu da kuma yawanm mutanen da za su kada kuri'a.

Yayin da ya tabbatar da cewar ba sa hasashen barkewar rikici ko samun tangarda a tsarin a yan kwanaki masu zuwa, jami'an hukumomin tsaro na shiri domin tabbatar da yin zabe cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel