Gwamnan PDP Ya Tsorata Kafin Ranar Zabe, Ya Kai Karar ‘Dan Takaran APC Wajen Buhari

Gwamnan PDP Ya Tsorata Kafin Ranar Zabe, Ya Kai Karar ‘Dan Takaran APC Wajen Buhari

  • Gwamna Bala Mohammed ya zargi Sadiq – Baba Abubakar da amfani da ‘yan daba wajen kamfe
  • Air Marshall Sadiq – Baba Abubakar mai ritaya shi ne yake takarar Gwamna a Jam’iyyar APC
  • A wasikar da Gwamnan Bauchi ya aika zuwa Shugaban kasa, ya nemi a cafke ‘Dan takaran APC

Bauchi - Bala Mohammed ya rubuta takarda yana mai kokawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan abokin hamayyarsa a zabe mai zuwa.

Premium Times ta ce Gwamna Bala Mohammed ya zargi Sadiq – Baba Abubakar mai neman takarar Gwamnan Bauchi a APC da neman kawo rikici.

A wata wasika da ya rubuta a ranar 10 ga watan Maris 2023, Mai girma Gwamnan ya ce yadda ‘dan takaran jam’iyyar APC yake kamfe yana da hadari.

Gwamnan mai neman tazarce a karkashin PDP ya zargi Sadiq – Baba Abubakar da yi wa mutane barazana, tada rikici da amfani da daba a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Kano, Kaduna da Jihohi 10 da Sai Gwamnoni, ‘Yan Takara Sun Yi Da Gaske a Zaben 2023

Ba haka PDP tayi kamfe ba

Mohammed ya ce jam’iyyarsa ta PDP tayi kamfe a duka kananan hukumomin Bauchi ba tare da an samu matsalar tsaro ba, akasin yadda APC ke kamfe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shi Sadiq – Baba yana yawo da tawagar jami’an tsaro da ‘yan daba da aka dauko daga jihohin waje domin su addabi ‘yan adawar siyasa da al’ummar gari.

Gwamnan Bauchi
Gwamnan Bauchi da Shugaba Buhari Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC
"Wannan ya yi sanadiyyar hallaka fiye da mutane uku da ba su ji ba-ba su gani ba, sannan dinbin mutane sun samu rauni a kananan hukumomin da ya ziyarta.
Ta’adin da ake yi wajen yawon yakin neman zaben ‘dan takaran APC ya jefa mutane a dar-dar, wannan ya tada hankalin jihar da aka sani da zaman lafiya."

- Gwamna Bala Mohammed

Rahoton ya ce wasikar Gwamnan ta kara da cewa abin da mutane suke tambaya shi ne yaushe za a kawo karshen wannan mummunan ta’adi da ake yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

Gwamnan ya ce garuruwan da APC ta jawo rikici akwai Akuyam, Misau, Akuyam da Alkaleri. A dalilin haka ya bukaci a cafke ‘dan takaran da mutanensa.

Mutanen Air Marshall

A cewar Bala, a tawagar ‘Dan takaran a lokacin akwai Yakubu Dogara, Yakubu Musa Abdullahi, Mallam Isah Yuguda da kuma Hon. Abdulmumin Kundak.

Takardar ta kara da cewa wani Bello Illela ne ake zargi da dauko hayar matasa domin su yi barna, kuma ‘dan takaran yana da Dogarai duk da ya bar gidan soja.

Tazarce da siyasar 2023

A wani rahoto da muka fitar a makon nan, kun ji Air Marshal Abubakar Siddique ya sha alwashin hana Bala Mohammed tazarce a jihar Bauchi a zaben 2023.

Haka zalika a Adamawa, Aisha Dahiru Binani ta tada hankalin Ahmadu Fintiri, sannan NNPP ta gigita Gwamna Inuwa Yahaya mai mulki APC a Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel