Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigai 5 a Kebbi

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigai 5 a Kebbi

  • Jam'iyyar PDP a jihar Kebbi ta shiga ruɗani mai girma bayan ta dakatar da manyan jiga-jiganta guda 7
  • A wata takarda da Sakataren PDP ya fitar, yace SEC ya amince da dakatar da tsoffin ministoci 2 da wasu mutum 5
  • Amma shugaban PDP a Kebbi, Usman Bello Suru, ya ce lamarin na cikin gida ne kuma zasu shawo kansa

Kebbi - Kwamitin zartaswa na jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ya amince da dakatar da tsoffin Ministoci biyu tare da wasu jiga-jigai 5 har sai baba ta gani bisa zargin cin amana da rashin ɗa'a.

Rahoton The Nation ya bayyana cewa tsoffin Ministocin da matakin dakatarwan ya shafa sun ne, Barista Kabiru Tanimu Turaki da Alhaji Buhari Bala.

Jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigai 5 a Kebbi Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Sakataren jam'iyyar PDP na jihar Kebbi, Abubakar Bawa Kalgo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Sakataren PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Maida Martani Mai Zafi

Ya kuma bayyana sunayen sauran mutane da PDP ta dakatar da, Haruna Saidu Dandio, Sani Bawa Argungu, Bala Abdullahi Dole Kaina, da Maryam Isah.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce dakatarwan zata fara aiki ne daga ranar Talata 14 ga watan Maris, 2023 kamar yadda kwamitin zartaswa da dattawan PDP na jiha suka amince.

Lamarin ya haifar da ruɗani

A wani abu da ya haddasa ruɗani, shugaban PDP na jihar Kebbi, Usman Bello Suru, ya bayyana matakin dakatar da jiga-jigan a matsayin mara amfani.

Bello ya faɗi haka ne yayin martani kan lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Ya ce abinda ya faru rigima ce ta cikin gida kuma nan ba da jimawa ɓa zasu shawo kan lamrin, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar ya tabbatar da cewa zasu magance duk abinda ke faruwa a cikin gida gabanin ranar zaben gwamna 18 ga watan Maris, 2023.

Dan takarar gwamna ya janye a Oyo

A wani labarin kuma Dan Takarar Gwamnan Oyo Na SDP Ya Janyewa Gwamna Makinde Mai Neman Tazarce

Yayin da ya rage saura kwanaki kalilan zaben gwamnoni a Najeriya, PDP mai mulki ta samu ƙarin karfi a jihar Oyo.

Dan takarar gwamna na Social Democratic Party ya hakura da neman zama gwamna, ya marawa gwamna mai ci baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel