Jamilu Gwamna Ya Karyata Batun Yi Wa Al’ummar Gombe Barazana Da Mutuwa

Jamilu Gwamna Ya Karyata Batun Yi Wa Al’ummar Gombe Barazana Da Mutuwa

  • Jigon APC a jihar Gombe, Jamilu Gwamna ya magantu a kan zarginsa da ake da yi wa yan Gombe barazanar kisa
  • Jamilu Gwamna ya ce sam shi bai taba yi wa wani barazana cewa sai dai uwarsa ta haifi wani idan bai zabi dan takarar jam'iyyarsa ba
  • A cewar gwamna abun da ya kai shi yankin Bolari shine nemawa Gwamna Inuwa Yahaya kuri'un al'umarsa a zaben da za a yi

Gombe - Jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Gombe, Jamilu Isyaku Gwamna, ya karyata zargin cewa ya yi barazanar illata mutanen gudunmar Bolari ta jihar Gombe idan suka ki zabar jam'iyyarsa.

Ku tuna cewa mutanen garin Bolari sun shigar da korafi ofishin yan sanda, suna masu zargin Gwamna da barazana ga rayuwarsu a yayin wani taro na siyasa a yankin.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan jihar Arewa ya sha jar miya, 8 cikin 13 na 'yan takarar gwamna sun janye masa

Jamilu Gwamna, jigon APC a Gombe
Jamilu Gwamna Ya Karyata Batun Yi Wa Al’ummar Gombe Barazana Da Mutuwa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sai dai kuma da yake hira da jaridar Daily Trust a ranar Talata, 14 ga watan Maris a garin Gombe, Gwamna ya karyata zargin.

Abun da na nema daga al'ummar Bolari, Jamilu Gwamna

Ya ce a matsayinsa dan yankin da ake ganin mutuncinsa, kawai ya je yankin ne don nemawa jam'iyyarsa kuri'u gabannin zaben gwamna mai zuwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daily Trust ta nakalto Jamilu Gwamna yana cewa:

"Na tara mutane don neman goyon bayansu ga jam'iyyata. Kuma na ce ya kamata mutane su fito don zabar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
"Ya kasance roko daga zuciya, kuma babu inda na ambaci cewa uwar wani za ta haifi waninsa. A yayin zaben karshe, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kawo yan daba wannan yankin, don haka kawai na gargade su cewa a wannan karon kada su kuskura su aikata haka saboda duk wanda ya zo kusa da akwatin zabe a wannan rana za a raba shi da yankin.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

"Kuma da kalmar Hausa na yi amfani don haka suka sauya fassarar ya zama cewa za a kashe su, wanda ba daidai bane."

Yan sanda na neman dan majalisa ruwa a jallo

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sanda ta bazama neman dan majalisa mai wakiltan mazabar Bauchi, Yakubu Shehu, ido rufe.

Ana dai neman Yakubu ne bisa zarginsa da hannu a kisan kai, hada baki, illata mutane da kuma ta da zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel