Jam’iyyar APC Na Ta Karban Lambobin Asusun Jama’ar Nasarawa Don Siyan Kuri’unsu

Jam’iyyar APC Na Ta Karban Lambobin Asusun Jama’ar Nasarawa Don Siyan Kuri’unsu

  • Masu ruwa da tsaki a jihar Nasarawa sun ce sun bankado shirin gwamnatin jihar na siyan kuri’u a zaben gwamnoni da ke tafe
  • Masu ruwa da tsakin sun kuma zargi gwamnatin jihar da kitsa rikici a gabanin zaben gwamnonin
  • Sun bukaci ‘yan jihar da su yi watsi da gwamnatin APC tare da zaban dan takarar gwamnan PDP, David Ombugadu

FCT, AbujaWasu jiga-jigan masu ruwa da tsaki na jihar Nasarawa sun bayyana cewa, jam’iyyar APC mai mulkin jihar za ta dungura a zaben da ke tafe.

Hakazalika, ta bayyana zargin cewa, gwamnatin jihar na shirin siyan kuri’u a zaben gwamna da ‘yan majalisun jiha da ke tafe nan kusa.

Wannan na fitowa ne daga taron manema labarai da suka hada, wanda wakilin Legit.ng ya halarta a ranar Laraba, 15 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yar Takarar Jam'iyyar APC Ta Yi Murabus Kwana 3 Gabanin Zabe, Asiri Ya Tonu

Gwamnan APC na shirin siyan kuri'u a Nasarawa
Jihar Nasarawa, mai makwabtaka da Abuja | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ana shirin kawo tsaiko ga zaben gwamna, inji masu ruwa da tsaki

Kwamared Manga David Ugbo, kakakin kungiyar masu ruwa da tsakin ya ce, gwamnan mai ci, Injiniya Abdullahi Sule ya kagu ya tabbatar da komawa mulki ko ta halin kaka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“APC a Nasarawa bata shirya yadda za ta lashe zaben gwamna na 18 ga watan Maris ba amma ta shirya satar nasara ta hanyar tashin hankali.
“Ta shirya ‘yan daba daga wajen jihar don taimaka mata wajen aiwatar da mugu kuma shaidanin nufinta ga al’ummar jihar Nasarawa, wadanda suka gaji da rashin tabuka komai na APC cikin shekarun hudu.”

Tawagar ta kuma zargi APC da kokarin cin zarafin ‘yan jihar, musamman a kananan hukumomin Karu, Keffi, Kokona, Akwanga, Nasarawa Toto da kuma birnin Lafia.

Hakazalika, sun yi zargin a halin yanzu gwamnatin jihar na tattarawa tare da karbar lambobin asusun bankin ‘yan jihar domin siyan kuri’unsu.

Kara karanta wannan

Abokin Gamin Atiku Ya Roki 'Yan Najeriya, Ya Maida Martani Kan Ci Gaba da Amfani da Tsoffin N500 da N1000

Daga karshe ta yi kira ga zaban dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP don tabbatar adalcoi ga al'ummar jihar.

Gwamnonin 5 na watakila ba za su yi tazarce ba a zaben gwamna na bana

A wani rahoton da muka tattaro muku, an bayyana gwamna Abdullahi Sule a cikin jerin gwamnonin da ka iya cin taliyar karshe a zaben bana.

Gwamnan, wanda ke neman wa’adi na biyu ya mulki ya kasance dan jam’iyyar APC, amma jiharsa ta gaza kawo kuri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan jiya.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da jiran zaben gwamnoni na ranar 18 ga watan Maris, inda za a zabi sabbi ko mayar da tsoffi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel